An Hukunta Mawakiya a Iran kan Rashin Saka Hijabi yayin Gudanar da Waƙa
- Kotun ɗaukaka ƙara a Iran ta tabbatar da hukuncin bulala 74 ga fitacciyar mawaƙiya Parastoo Ahmadi, bayan ta yi waƙa ba tare da hijabi ba
- Ahmadi mai shekara 29 ta yi wasan kwaikwayo sanye da riga mara hannun riga a watan Disamba 2024, lamarin da ya bazu sosai
- Kotun farko ta Qom ta same ta da wasu mutane takwas da laifi, yayin da kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Kotun ɗaukaka ƙara a Iran ta tabbatar da hukuncin bulala 74 da aka yanke wa fitacciyar mawaƙiya Parastoo Ahmadi, bayan ta yi waƙa ba tare da hijabi ba.
Ahmadi, mai shekara 29, ta yi wani wasan kwaikwayo sanye da riga mara hannun riga, wanda ta watsa kai tsaye a tashar YouTube dinta a watan Disamba 2024. Bidiyon ya bazu kuma ya samu miliyoyin kallo.

Source: UGC
Dokar Iran ta bukaci mata su rufe gashin kansu tare da sanya tufafin da suka dace a bainar jama'a. Haka kuma, an haramta wa mata yin wasan kwaikwayo a bainar jama'a, cewar The Guardian.
Hukumomin shari'a a Iran sun fara shari'ar Ahmadi bayan wasan kwaikwayon, suna bayyana cewa abin ya saba wa dokoki da ƙa'idojin al'adun ƙasar.
A watan Yuni, wata kotun laifuka da ke Qom ta samu Ahmadi da wasu mutane takwas daga cikin ƙungiyar waƙarta da masu shirya wasan da laifukan da suka haɗa da "cin zarafin tarbiyyar jama'a" ta hanyar wallafa abubuwan da suka shafi batsa da rashin kunya.
An yanke musu hukuncin bulala 74, hana su gudanar da ayyukan sauti da bidiyo na tsawon shekaru biyu, sannan aka hana su fita daga ƙasar na tsawon shekaru biyu.
Lauyoyinsu sun ce wata babbar kotu ta yi watsi da ƙarar da suka shigar ranar Juma'a ba tare da gudanar da zaman sauraron ƙarar ba.
Ɗaya daga cikin lauyoyin ya shaida wa BBC cewa, a ganinsu, gudanar da wasan kwaikwayon ba laifi ba ne.
Ya ce kotun farko ta yi amfani da ɗaya daga cikin hukuntuka mafi tsauri, duk da cewa akwai tara da wasu hukuntuka marasa tsanani.
Lauyan ya ƙara da cewa kotun ɗaukaka ƙarar na da damar gudanar da sauraron ƙara, amma ba ta yi hakan ba, sannan ta tabbatar da hukuncin. Ya ce hakan na iya zama domin hana sake faruwar irin wannan lamari.
Mawaƙiyar da ke gudun hijira, Googoosh, ta yi kira da a kawo ƙarshen abin da ta bayyana a matsayin kwanakin duhu.
Mawaƙi Hossein Alizadeh ya ce a shirye yake ya sha bulala 70 a madadin Parastoo Ahmadi. Kungiyar Amnesty International ma ta soki hukuncin.
Amnesty International ta bayyana cewa bulala wani nau'in hukunci ne mai tsanani, na wulakanci da cin zarafi, wanda ya saba da cikakken haramcin azabtarwa da sauran munanan mu'amala.
Iran ta gargadi Trump a yakinta da ƙasar
Mun ba ku labarin cewa Kakakin Jami’an Tsaron Juyin Juya Hali na Iran ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da yin ƙarya kan makaman nukiliya.

Kara karanta wannan
El Rufai ya aika sako ga 'yan uwa da abokan arziki bayan shafe fiye da kwanaki 200 a tsare
Hosein Mohebbi ya ce Amurka ta gaza a yaƙin soji da Iran, yana mai cewa ya kamata Washington ta fice daga yankin Gabas ta Tsakiya.
Kakakin ya ce ya kamata a sanar da jama’ar Amurka gaskiyar abin da ya faru domin bambance karya da gaskiya.
Asali: Legit.ng

