Malaman da aka Sace a Hanyar zuwa Yi wa Tinubu Addu'a Sun Shafe Mako 2 a Daji

Malaman da aka Sace a Hanyar zuwa Yi wa Tinubu Addu'a Sun Shafe Mako 2 a Daji

  • An shafe mako biyu da satar wasu limaman Juma’a shida a Jihar Zamfara, amma har yanzu ba a san inda suke ba balle a ceto su
  • An yi garkuwa da limaman ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara domin halartar addu’a ta musamman ga Bola Tinubu
  • ’Yan uwan limaman sun ce suna fama da damuwa yayin da suke ƙoƙarin biyan kuɗin fansar da ’yan bindigar suka nema domin ganin an sako su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara – Mako biyu bayan da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da limaman Juma’a shida a Jihar Zamfara, har yanzu ba a samu labarin inda suke ba.

An sace limaman ne a ranar 13 ga Satumba, lokacin da suke tafiya zuwa Talata Mafara domin halartar wata addu’a ta musamman da aka shirya domin nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Matsin da ake ciki yana damun Tinubu, ya fadi hanyar tsame mutane miliyan 5 daga talauci

Malaman jihar Zamfara
Wasu malamai a wajen yi wa Bola Tinubu addu'a a Zamfara. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa an yi garkuwa da su ne a Gidan Suleiman Bature, kimanin kilomita uku daga ƙauyen Damri.

Iyalai sun shiga cikin damuwa

Ɗan wani limami da aka yi garkuwa da shi ya shaida wa Trust Radio cewa iyalai da al’ummomin da lamarin ya shafa suna ƙoƙarin biyan kuɗin da ’yan bindigar suka nema.

Ya ce rashin sanin halin da limaman suke ciki ya jefa iyalai da al’ummomin cikin tsananin damuwa.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin al’ummomin sun fara neman wasu hanyoyin da za su bi wajen ganin an saki limaman, yana mai cewa suna ganin ba a samu isasshen taimako daga gwamnati da hukumomin tsaro ba.

Ya kuma ce wasu mutane sun fara yin kalamai da ke alakanta sace limaman da dalilin tafiyarsu, abin da ya ce yana ƙara wa iyalan da ke cikin damuwa ciwo.

An sauya masu wuri

Kara karanta wannan

An kama matasa 2 kan kashe uwa mai 'ya'ya 5 yayin satar waya a Gombe

Wani ɗan uwan limaman, wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ’yan bindigar sun kwashe limaman zuwa wani wuri da ba a san inda yake ba.

Ya ce al’ummomin sun rasa tabbacin samun taimako daga wani ɓangare tun bayan da aka sanar da su cewa an tafi da limaman zuwa wani sabon wuri.

A cewarsa, bayan tattaunawa kai tsaye tsakanin ’yan bindigar da wakilan al’ummomin, an rage kuɗin fansar daga N100m zuwa N30m.

Taswirar jihar Zamfara
Taswirar jihar Zamfara a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Ya ce tattaunawar ta yi zafi lokacin da ɗaya daga cikin masu shiga tsakani ya yi tayin N15m, amma daga bisani aka amince da N30m bayan wasu daga cikin ’yan bindigar sun roƙi shugaban ƙungiyar.

Sunayen limaman da aka sace

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani mazaunin ɗaya daga cikin al’ummomin da lamarin ya shafa ya ce an sace limaman ne yayin da suke amsa gayyatar Sanata Abdul’aziz Yari zuwa Talata Mafara domin halartar addu’a ta musamman.

Ya bayyana limaman da suka haɗa da Malam Shehu, limamin Masallacin Juma’a na Dakko; Liman Yahuza, limamin Dogon Madacci da mataimakinsa; Liman Bala na Fagon; da Na’ibi Tasi’u na Tungar Nagodai.

A bayanin da ya yi, ya ce dukkansu ’yan asalin ƙaramar hukumar Bakura ne, sai Na’ibi Tasi’u wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Anka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng