Yadda Najeriya Ta Fara Shirin Kera Makamai da Motoci Masu Sulke

Yadda Najeriya Ta Fara Shirin Kera Makamai da Motoci Masu Sulke

  • Najeriya za ta fara kera motocin yaƙi masu sulke da na’urorin dakile jiragen sama marasa matuƙi a cikin ƙasar domin ragargazar yan ta'adda
  • Haɗin gwiwar da aka kulla da wani kamfanin tsaron Masar zai taimaka wajen musayar fasaha tare da samar da ayyukan yi ga ’yan Najeriya
  • DICON-D7G na shirin gina tashar jiragen ruwa ta musamman a Legas domin sauƙaƙa jigilar kayan aikin soji da albarkatun da ake amfani da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano –Shugaban Kamfanin Masana’antun Tsaron Najeriya, DICON-D7G Osman Chennar, ya ce Najeriya na shirin fara samar da motocin yaƙi masu sulke.

Haka kuma kasar zan za ta fara kera na’urorin dakile jiragen sama marasa matuƙi da sauran kayayyakin soji na musamman a cikin gida.

Kara karanta wannan

Maganin mallaka: Matashin da ya birne Kur’ani da wasu kayan tsubbu ya shigo hannu

Najeriya ta yi sabon shiri kan yan ta'adda
Bello Matawalle tare da wasu sojojin Najeriya Hoto: Bello Mawalle
Source: Twitter

The Guardian ta wallafa cewa Chennar ya bayyana hakan ne yayin da yake bayani kan sakamakon rangadin kwanaki biyu da wata tawaga karkashin jagorancin karamin Ministan Tsaron, Bello Matawalle, ta kai masana’antu da cibiyoyin kera kayan aikin soji a birnin Alkahira na ƙasar Masar.

Shirin Najeriya kan rashin tsaro

Aminiya ta wallafa cewa ya ce shirin da ake aiwatarwa tare da haɗin gwiwar Eagles International for Defence Systems zai taimaka wajen musayar fasaha, faɗaɗa ƙarfin Najeriya na kera kayan aikin tsaro a cikin gida da kuma samar da ɗaruruwan guraben ayyukan yi.

Yan ta'adda za su gamu da fushin sojin Najeriya
Wasu daga cikin yan ta'adda a Najeriya Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

A cewarsa, haɗin gwiwar zai samar da ayyukan yi ga sama da ma’aikata 200, tare da ba da damar samun ayyukan yi ga kusan tsoffin jami’an soji 100.

Chennar ya ce tawagar ta duba nau’o’in kayan aikin soji da tsarin samar da su daban-daban, waɗanda za su taimaka wa Najeriya wajen cimma burinta na ƙara ƙarfin masana’antar tsaro ta cikin gida.

Kara karanta wannan

Bello Matawalle ya je wajen kera makamai a Masar, ana neman haɗaka da Najeriya

Yarjejeniyar Najeriya da cibiyar Masar

Ya ce yarjejeniyar za ta bai wa Najeriya damar samun fasahohin zamani na tsaro tare da gina ƙarfin kera nau’o’in motocin yaƙi da sauran kayan aikin soji a cikin gida, sannan nan gaba a iya fitar da su zuwa wasu ƙasashen Afrika.

Daga cikin motocin da ake shirin samarwa akwai mota mai sulke kirar BR6, da kuma ɗakin harba harsashin turmi mai milimita 120.

Haka kuma akwai motocin jigilar marasa lafiya da motocin ɗaukar waɗanda suka jikkata, da MRAP-Buffalo U.10 da M.12, MRAP-Buffalo F-4 da Rhino Guard GXR mai kariya daga jiragen sama marasa matuƙi.

Shirin ya zo ne yayin da Najeriya ke ƙara ƙoƙarin rage dogaro da shigo da kayan aikin soji daga ƙasashen waje, a daidai lokacin da matsalolin tsaro ke ci gaba da addabar sassa daban-daban na ƙasar.

An kama masu kerawa yan ta'adda makamai

A baya, mun wallafa cewa rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun tarwatsa wata haramtacciyar cibiyar ƙera makamai a wani yanki na jihar Kebbi da ke Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Kamfanoni da mutane 9 da SEC ta ƙaƙabawa takunkumi

Yayin da aka kai farmaki masana'anatar, sojoji sun ƙwato bindigogi biyar da aka ƙera a cikin gida masu kama da makamai masu hadari kamar bindigun AK-47 tare da kama mutum biyu

Jami'an tsaro sun fara ƙarin bincike da samame domin cafke sauran waɗanda ke da hannu a cibiyar da kuma dakile safarar makamai a jihar wanda ake amfani da su wurin kai hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng