Ana Batun Rashin Lafiya, Onanuga Ya Fadi Halin da Tinubu ke Ciki a Faransa
- Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Shugaba Bola Tinubu yana cikin ƙoshin lafiya duk da rashin ganinsa a Abuja da taron Majalisar Ɗinkin Duniya
- Fadar ta ce Tinubu yana hutu na shekara-shekara ne, amma yana ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati daga ƙasar waje
- Ta kuma bayyana cewa Shugaban Ƙasar zai dawo Najeriya a wannan makon domin halartar bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Fadar Shugaban Ƙasa ta yi karin haske kan rashin ganin Shugaba Bola Tinubu a Abuja da kuma rashin halartarsa taron Majalisar Ɗinkin Duniya a New York.
Fadar ta ce Tinubu yana cikin ƙoshin lafiya, yana kuma ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati yayin da yake hutun shekara-shekara a ƙasar waje.

Kara karanta wannan
"Ka ba mutane hakuri," Atiku ya sake tono abin da Bola Tinubu ya aikata a Najeriya

Source: Facebook
Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi.
Dalilin rashin Tinubu a Abuja
Onanuga ya ce Tinubu yana hutun shekara-shekara ne, amma hutun nasa na aiki ne, don haka yana da cikakken damar yin hakan yayin da yake ci gaba da kula da ayyukan ƙasa.
Ya ce a wannan zamani na fasahar sadarwa, ba lallai ne Shugaban Ƙasa ya kasance a Abuja a zahiri ba kafin ya iya gudanar da ayyukan da aka zaɓe shi domin yi.
Fadar ta ce Tinubu ya ci gaba da gudanar da ayyukansa daga ƙasar waje, inda ta kawo ganawarsa da masu zuba jari a Faransa a matsayin misali.
Dalilin rashin Tinubu a UNGA
Fadar Shugaban Ƙasa ta kuma mayar da martani kan sukar da aka yi wa Tinubu saboda rashin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya a New York.
Ta ce wasu manyan shugabannin Afirka, ciki har da Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da Shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi, su ma ba su halarci taron ba.
Fadar ta ce Tinubu ya sanar da hutun shekara-shekara tun farko, sannan ya ba Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima damar wakiltar Najeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya.
Martanin Fadar kan Peter Obi
Fadar Shugaban Ƙasa ta kuma soki tsohon Gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, kan tambayar inda Tinubu yake.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa ta ce Obi yana yin kamar bai san inda Shugaban Ƙasar yake ba, duk da bayanan da aka bayar kan hutun Tinubu.
Fadar ta ce ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya a wannan makon, gabanin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.
Ta kuma ce ana sa ran zai halarci bikin ƙaddamar da wani fim da aka shirya kan rayuwar marigayi ɗan kasuwa kuma mai fafutukar dimokuraɗiyya, MKO Abiola, a Legas.
Tinubu na namen tazarce
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa tana gyara kura-kuran gwamnatocin da suka gabata, tare da neman ƙarin lokaci domin kammala ayyukan da ta fara.
Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Juma'a ta bakin Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, yayin wata addu'a ta musamman da aka gudanar a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
Shugaban Ƙasar ya ce zaman lafiya da ci gaba suna dawowa Najeriya a hankali, yana mai cewa tafiyar ƙasar tun bayan samun ’yancin kai ta kasance cike da nasarori da kuma ƙalubale.
Asali: Legit.ng

