Sanusi II Ya Yi Magana kan El Rufa'i da Yadda ake Zalunci a Najeriya
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce mutum na iya aikata kusan komai a Najeriya ya kuɓuta idan yana da alaƙar siyasa mai ƙarfi
- Sanusi II ya ce akwai hukumomi da kotuna da aka kafa domin yaƙi da cin hanci, amma yadda ake aiwatar da dokokin na iya fuskantar tasirin siyasa
- Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma matsalar dukiyar da ba a iya bayyana tushenta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos – Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce mutum na iya aikata komai a Najeriya ya kuɓuta daga hukunci idan yana da alaƙar siyasa da ta dace.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da tattaunawa kan abokin Sarkin kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Source: Twitter
Sanusi II ya bayyana hakan ne a wata hira da Channels Television a Lagos yayin gabatar da wani littafi mai juzu’i uku da lauya mai yaƙi da cin hanci, Dr Wahab Shittu (SAN), ya rubuta.
Maganar Sanusi II kan dokoki
Sanusi II ya ce duba dokokin da ake da su domin gano muhimmancin aiki da su da magance matsalar dukiyar da ba a bayyana tushenta ba abu ne mai muhimmanci.
Sai dai ya jaddada cewa ba wai sake duba dokoki kaɗai ake buƙata ba, har ma da inganta yadda hukumomin da ke da alhakin aiwatar da su ke amfani da su.
Ya ce Najeriya tana da hukumomi da kotuna da aka kafa domin ganowa tare da gurfanar da mutanen da ake zargi da cin hanci da rashawa.
Alakar siyasa da shari’o’i
Sanusi II ya ce akwai lokutan da ake zargin wasu mutanen da ke fuskantar tuhumar cin hanci da rashawa ana watsar da ƙararrakinsu saboda irin alaƙar siyasar da suke da ita.
Ya ce irin wannan yanayi na iya sa jama’a su fara tambayar ko ana yaƙi da cin hanci da rashawa ne da gaske ko kuma ana amfani da shari’a wajen gudanar da rikicin siyasa.
Batun Nasir El-Rufa'i
Sanusi II ya kawo batun tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, a matsayin misali na abin da ya ce na iya haifar da irin wannan tambaya.
Ya ce El-Rufai ya shafe watanni a tsare ba tare da an same shi da laifi ba, yana mai tambayar ko irin wannan lamari yana cikin yaƙi da cin hanci ko kuma yana da alaƙa da siyasa.

Source: Facebook
Sai dai bayanan kotuna sun nuna cewa El-Rufai na fuskantar shari’o’i daban-daban, ciki har da tuhumar da DSS ta shigar kan zargin kutse a sadarwar waya, kuma an ci gaba da sauraron shari’ar.
Ga bidiyon da ya yi bayani:
Magana kan malaman addini
A wani labarin, mun ruwaito cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a samu ƙarin bambanci tsakanin harkokin addini da siyasa.
Sanusi II ya ce ya kamata malaman addini su mayar da hankali kan ayyukan da suka shafi addini, yayin da ’yan siyasa su mayar da hankali kan gudanar da mulki.
Ya bayyana cewa ’yan siyasa suna da alhakin samar da ilimi, kiwon lafiya da inganta tattalin arziki, ba wai ɗaukar nauyin harkokin addini ba.
Asali: Legit.ng

