Gwamna Ya Fitar da Sanarwa, Ya Hana Bikin Ranar Samun Yancin kan Najeriya

Gwamna Ya Fitar da Sanarwa, Ya Hana Bikin Ranar Samun Yancin kan Najeriya

  • Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya dakatar da bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya da aka shirya gudanarwa a ranar Alhamis
  • Wannan mataki da aka dauka ya fara aiki nan take daga ranar Litinin, 28 ga Satumba, 2026 kamar yadda gwamnatin Kaduna ta sanar
  • Gwamnatin jihar ba ta bayyana dalilin dakatar da bikin ba a daidai lokacin da yan Najeriya ke shirin murnar ranar yancin mai ta bana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani ta sanar da dakatar da bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya, wanda aka shirya gudanarwa a ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026.

Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai da Al’adu, Ahmed Maiyaki, ne ya sanar da dakatarwar a madadin Gwamna Sani a ranar Talata, 28 ga watan Satumba, 2026.

Kara karanta wannan

Sanata Barau ya kori hadimarsa 'yar Kannywood daga mukaminta

Malam Uba Sani.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani yana jagorantar taron Majalissr zartarwa Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kwamishinan yada alabaran na Kaduna ya ce gwamnati na nadamar duk wata matsala da matakin zai iya jawo wa jama’a.

Ya ce matakin ya fara aiki ne daga ranar Litinin, 28 ga watan Satumba, 2026, yana mai kira ga mazauna Kaduna da su bi foka sau da kafa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata mai taken, “Dakatar da Bikin Cika Shekaru 66 da Samun ’Yancin Kan Najeriya”, Maiyaki ya ce:

“Wannan sanarwa ce ga jama’a cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta dakatar da bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya, wanda aka shirya gudanarwa a ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026.
“Dakatarwar ta fara aiki nan take, daga ranar Litinin, 28 ga Satumba, 2026.”

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin jihar na nadamar duk wata matsala da wannan mataki zai iya haifarwa, tare da godiya ga jama’a da duk masu ruwa da tsaki bisa hadin kai, fahimta da goyon bayan da suke bai wa gwamnati.

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu kan karbo bashin kusan Naira tiriliyan 2

Sai dai gwamnatin Gwamna Sani ba ta bayyana wani dalili na dakatar da bikin ba.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262