Abubuwa 6 da Ya Kamata a Sani game da Gidauniyar Tsaro da Gwamnonin Arewa 19 Suka Kaddamar

Abubuwa 6 da Ya Kamata a Sani game da Gidauniyar Tsaro da Gwamnonin Arewa 19 Suka Kaddamar

Kaduna, Nigeria - A makon jiya kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya da majalisar sarakunan gargajiya suka gudanar da taron hadin gwiwa a gidan gwamnatin jihar Kaduna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Taron dai ya maida hankali ne kan matsalolin da suka addabi 'yankin Arewacin Najeriya musamman matsalar tsaro tare da nazari kan matakin da ya kamata a dauka.

Taron Arewa.
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya tare da Mai alfarma Sarkin Musulmi a taron hadin gwiwa da aka yi a Kaduna Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Mai masaukin baki kuma gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya tabbatar da hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook bayan kammala taron.

Gwamnonin Arewa sun kaddamar da gidauniya

Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da aka gudanar a wannan taro shi ne kaddamar da gidauniyar da yaki da matsalar tsaro a Arewa.

Gwamnonin jihohi 19 sun amince za su rika tara Naira biliyan 1 a kowane wata domin gudanar da ayyukan wannan gidauniya, wacce za ta maida hankali wajen dawo da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren tura wa wani mutum kudin fanshon miliyoyi

A taron, an kafa kwamitin da zai jagoranci wannan gidauniya, wanda ya kunshe wakilai daga kowace jiha tare da sarakuna.

Gwamnonin sun buƙaci jihohin Arewa, sarakuna, ƙungiyoyin fararen hula da kafafen yaɗa labarai su mutunta kwamitin tare da ba shi haɗin kan da ya dace domin aikinsa na lalubo hanyoyin inganta tsaro a yankin.

Muhimman ayyukan gidauniyar Arewa

A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku muhimman ayyukan da gidauniyar za ta maida hankali kansu domin farfado da yankin Arewa da matsalar tsaro ta yi wa katutu.

1. Tara ƙudi da kula da su

Wannan gidauniya karkashin shugabancin kwamaitin da gwamnonin Arewa suka kafa, ita ke da alhakin tara kudin da aka amince da su a kowane wata tare da tafiyar da su yadda ya kamata.

Rahoton BBC Hausa ya nuna cewa gwamnoni sun amince su riƙa bayar da Naira biliyan ɗaya duk wata ga gidauniyar tsaron, don haka mambobin kwamitin za su riƙa kula da kuɗaɗe tare da aiwatar da yadda aka tsara kashe su.

Arewa.
Mambobin kwamitin gidauniyar tsaro lokacin da kungiyar gwamnonin Arewa ta rantsar da su a Kaduna Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

2. Tallafa wa jami'an tsaro

Kara karanta wannan

Masanin da ya yi tsayuwar daka yana kare Musulunci a Amurka ya rasu

Ɗaya daga cikin muhumman ayyukan wannan gidauniya shi ne tallafa wa jami'an tsaro da kayan aiki domin tunkarar duk wata barazana daga 'yan ta'adda da sauran miyagu.

Gidauniyar za ta rika amfani da kudaden da gwamnonin Arewa suka tara wajen sayen kayan aiki kamar na leken asiri da makaman yaƙi don taimakawa jami'an tsaro.

A rahoton Premium Times, gwamnonin sun bayyana cewa hakan zai warware giɓin karancin kayan aikin da dakaru ke fuskanta kuma ya taimaka masu wajen dawo da zaman lafiya a Arewa.

3. Hadin kai tsakanin jihohin Arewa

Kwamitin da aka kafa domin jagorantar wannan gidauniya ya kunshi wakilai daga kowace jiha daga cikin jihohin Arewa 19, kamar yadda jaridar Punch ta kawo.

Kwamitin zai gudanar da ayyukansa ne ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mahmoud Yayale Ahmed, CFR daga jihar Bauchi da Janar Martin Luther Agwai, CFR (mai ritaya), tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, daga Kaduna.

Gwamnoni sun ɗora wa wannan kwamiti alhakin aiki tare da musayar bayanai domin magance matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.

Ana sa ran gidauniyar za ta hada kan jihohi wajen gudanar da ayyukan tsaro cikin hadin kai musamman kula da iyakokinsu.

Kara karanta wannan

Bauchi: Bala Mohammed ya yi garambawul a majalisar zartarwa, ya sauke kwamishinoni 2

Taron Arewa.
Gwamnoni da wakilan jihohi a taron hadin gwiwa kan tsaro da aka gudanar a Kaduna Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

4. Magance tushen matsalar tsaro

Ɗaya daga cikin abubuwan masu ruwa da tsaki da sharhi kan harkokin tsaro ke kiraye-kiraye a kansa shi ne lalubo tushen matsalar tsaro da kuma magance ta.

Ana ganin idan har aka lalubo asalin matsalolin da suka haifar da ayyukan yan bindiga da sauran kungiyoyin ta'addanci kuma aka magance su, to zaman lafiya na iya dawowa a Arewa.

Bisa haka ne gwamnonin suka dora wa kwamitin da zai jagoranci wannan gidauniya alhakin hada kai da duka masu ruwa da tsaki domin zakulo tushen matsalar tsaron Arewa da tsara yadda za a magance su.

Rahoton This Day ya nuna cewa ana sa ran gidauniyar za ta haɗa kai da sarakunan gargajiya da shugabannin al'umma da masu ruwa da tsaki domin magance abubuwan da ke janyo tashin hankali.

5. Taimaka wa yan sa-kai

Bugu da kari, gidauniyar za ta hada kai da dakarun rundunonin 'yan sa-kai da ke jihohin Arewa domin karfafa su da kara masu kwarin gwiwa wajen magance matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

An yi kicibis, sojoji sun yi ram da 'dan bindiga a hanyar sintiri

Gwamnonin sun ce gidauniyar za ta karfafa yan sa-kai ta hanyar samar masu da kayan aiki da kula fa walwalarsu, wanda zai kara masu kwarin gwiwar taimaka wa jami'an tsaro, cewar tashar Channels tv.

6. Hada kai da Gwamnatin tarayya

Haka nan kuma gwamnonin Arewa sun bayyana cewa gidauniyar za ta hada kai da hukumomin gwamnatin tarayya da harkar tsaro ta shafa domin su yi aikin cikin hadin kai.

A cewarsu, gidauniyar za ta yi aiki kafada da kafada da Gwamnatin tarayya domin tallafawa jami'an tsaro da yan sa-kai na jihohi, da nufin kawo karshen tashe-tashen hankula a Arewa.

Gwamnonin Arewa.
Gwamnoni da sarakunan Arewa a taron da suka gudanar a jihar Kaduna Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Arewa za ta amfana da yan sandan jihohi

A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu na kafa rundunar 'yan sandan jihohi.

Barau Jibrin ya ce hakan wata muhimmiyar dabara ce na ƙarfafa tsarin tsaro tare da taimakawa wajen magance matsalar rashin tsaro, musamman a Arewacin Najeriya.

Ya bayyana cewa jami'an rundunar za su fito ne daga al'ummomin da za su yi aiki a cikinsu, lamarin da zai taimaka wajen yaƙi da 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262