‘Babu Kamar Shi’: An Fadi Bangaren da Tinubu Ya fi Sauran Shugabannin Najeriya
- Wani jgon APC, Isaac Balami ya bayyana dalilin barin tafiyar Obidient karkashin masu goyon bayan Peter Obi
- Balami ya ce ya koma APC ne bayan ya gamsu cewa gwamnatin Bola Tinubu ta fara magance wasu matsaloli
- Tsohon mataimakin daraktan kamfen na Obi-Datti ya ce LP ta kasa kare kuri'un da ta samu a kotu saboda rashin tsari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon mataimakin daraktan kamfen na Obi-Datti kuma jigo a APC, Isaac Balami ya magantu kan salon mulkin Bola Tinubu.
Ya bayyana cewa bai ga wata makoma a cikinta ba, yana mai cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar masa da kuskuren da ya yi lokacin da yake adawa da shi.

Source: Twitter
Da yake magana a shirin ARISE NEWS, Balami ya ce ya yi wa Tinubu suka masu tsanani a baya, amma daga baya ya fahimci cewa shugaban ya yi abin da ya sa ya canja ra'ayinsa.
Yadda Balami ya hakura da APC a 2022
Balami ya bar APC a watan Satumbar 2022 domin shiga jam'iyyar Labour mai adawa da tafiyar Obidient.
A cewarsa, ya dauki wannan mataki ne saboda damuwarsa kan batun tikitin Musulmi da Musulmi da kuma abin da ya kira nuna wariya ga wasu kabilu.
Sai dai ya koma APC a watan Yulin 2024 bayan rikicin cikin gida da ya dabaibaye LP, ya ce babu laifi mutum ya amince cewa wanda ya saba wa ya tabbatar masa da gaskiya.
Ya musanta zargin cewa ya ci amanar magoya bayan Obidient, yana mai cewa barinsa APC a shekarar 2022 zabinsa ne.
Ya kara da cewa kamar yadda APC ta karbe shi lokacin da ya fita, haka ya kamata a mutunta zabinsa na komawa jam'iyyar.
Ya ce:
“A tarihin dimokuraɗiyya tun daga shekarar 1999, babu wani shugaban ƙasa da ya goyi bayan kabilu marasa rinjaye tare da yi musu adalci a Najeriya kamar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”

Kara karanta wannan
Atiku da Peter Obi sun tafka kuskure, an cire su daga barazanar da Tinubu zai fuskanta a 2027

Source: UGC
Sadaukarwar da Balani ya yi ga Obi
Balami ya bayyana cewa ya sadaukar da lokaci da dukiyarsa wajen yakin neman zaben Peter Obi da Datti Baba-Ahmed.
Ya ce ya taimaka wajen tara kungiyoyin goyon baya da horas da jami'an zabe, amma jam'iyyar ba ta nuna isasshen sha'awa wajen tabbatar da tsari ba.
A cewarsa, jam'iyyar Labour ta kasa samar da isassun jami'an zabe da takardun sakamakon zabe domin kare kuri'un da ta samu a kotu.
Ya ce wannan gazawar ce ta sa ya yanke shawarar ba zai ci gaba da zama cikin tsarin da ba shi da karfi ba.
Balami ya yabawa gwamnatin Tinubu kan sauye-sauyen da take aiwatarwa, ciki har da cire tallafin mai, aiwatar da cin gashin kan kananan hukumomi da kuma kokarin jawo jarin kasashen waje. Ya ce wadannan matakai sun sa ya sake duba matsayinsa.
Tinubu ya yi waya da gwamnan Osun

Kara karanta wannan
Malamin addini ya tubure kan dokar gwamnatin Tinubu na hana wa'azi, ya sha alwashi
An ji cewa shugaba Bola Tinubu ya kira gwamnan Osun, Ademola Adeleke, inda ya tabbatar masa cewa ya ba hukumar EFCC umarci kan rufe da asusun gwamnatin jihar.
Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa Tinubu ya ba EFCC umarni ta dauki matakan soke umarnin kotun da ya hana amfani da asusun.
Matakin daskarar da asusun ya jawo ce-ce-ku-ce, inda masu suka ke zargin cewa yana da alaka da zaben gwamnan Osun da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.
Asali: Legit.ng
