Yaki da ta'addanci a Najeriya
An kashe wani fitaccen shugaban dabar ’yan bindiga, Kachalla Mu’azu, da wasu manyan yaransa shida a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma a fadan gaba.
Yan bindiga sun kashe wani shugaban matasa kuma tsohon shugaban Berom Youth Moulders-Association (BYM) na Gashish a jihar Filato, Rwas Paul Danladi.
Wata mata, Sumaiya Abubakar ta amsa laifin taimaka wa ’yan kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta hanyar ajiye musu makamai da alburusai a jihar Nasarawa.
Akalla sojoji 12 da fararen hula biyar ne aka kashe, yayin da ’yan bindiga sun kai hari wani sansanin sojoji a ƙauyen Bindin, ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
An kashe Fasto da mutane 27 a hare-haren da aka kai sassan Plateau cikin mako guda, duk da dokar hana fita daga magariba zuwa safiya da gwamnatin jihar ta kakaba.
’Yan Sandan Najeriya sun kama mutane 96 da ake zargi da laifuka tare da kuɓutar da mutane 42 da aka yi garkuwa da su a samamen da suka gudanar a faɗin ƙasar.
Fasto Ezekiel Dachomo ya ziyarci Isra’ila domin yi wa Najeriya, Tinubu, Mutfwang da Netanyahu addu’a, bayan zargin rasa ’yan uwansa tara a harin Plateau.
Dan majalisar Amurka Riley Moore ya yaba da rahoton kama Mahmoud Adam, yana danganta lamarin da hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da kasar Amurka.
Kasar Najeriya da takwararta ta Amurka sun ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar sojoji wajen yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri da inganta tsaron iyakoki.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari