Gwamnoni 19 da Manyan Sarakunan Arewa Sun Cimma Matsaya kan Kafa Yan Sandan Jihohi

Gwamnoni 19 da Manyan Sarakunan Arewa Sun Cimma Matsaya kan Kafa Yan Sandan Jihohi

  • Gwamnonin jihohin Arewa 19 da sarakuna sun amince da kara hadin gwiwa wajen magance matsalar tsaro da ta addabi yankinsu
  • A taron da suka gudanar a Kaduna, sun yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen yaki da rashin tsaro
  • Gwamnoni da sarakunan Arewa sun kuma tabbatar da cikakken goyon bayansu ga shirin kafa 'yan sandan jihohi domin inganta tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Gwamnonin jihohin Arewa 19 tare da sarakunan gargajiya sun sake jaddada kudirinsu na kara hada kai domin magance matsalar rashin tsaro.

An cimma wannan matsaya ne bayan taron hadin gwiwa da suka gudanar ranar Laraba a Sir Kashim Ibrahim House da ke Kaduna, inda suka yi nazari kan tabarbarewar matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya kausasa murya kan 'yan bindiga, ya ce a hada kai a yake su

Taron Arewa.
Gwamna Uba Sani, Gwamna Inuwa Yahaya da Mai Alfarma Sarkin Musulmi a taron manyan Arewa da aka gudanar a Kaduna Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ne ya sanya hannu kan sanarwar bayan taron, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A cewar sanarwar, mahalarta taron sun tattauna hanyoyin da suka dace kuma masu dorewa na magance matsalar tsaro bayan tuntubar manyan jami'an tsaro daga sassa daban-daban na Arewa.

Gwamnoni da sarakuna sun yabawa Tinubu

Kungiyar ta yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bai wa harkokin tsaro muhimmanci, tare da sake bayyana goyon bayanta ga kokarin gwamnatin tarayya na dawo da zaman lafiya a fadin Najeriya.

Ta kuma yi alkawarin kara karfafa musayar bayanan sirri, gina juriyar al'umma da samar da tsarin hadin gwiwar yanki domin tabbatar da tsaro da ci gaban tattalin arziki.

Sun goyi bayan kafa 'yan sandan jihohi

Gwamnonin da sarakunan sun bayyana cewa matsalar tsaro a Arewa na bukatar daukar matakai cikin gaggawa tare da hadin kai.

Sun yi maraba da ci gaban da aka samu wajen shirin kafa 'yan sandan jihohi, tare da yabawa Shugaba Tinubu da Majalisar Dokoki ta Kasa kan kokarin gyaran kundin tsarin mulki da ake yi domin hakan ya tabbata.

Kara karanta wannan

Abba Kabir da gwamnonin APC da ke neman tazarce sun fadi matsayarsu kan Tinubu

A cewarsu, idan aka horas da jami'an yadda ya kamata tare da samar musu da kayan aiki da tallafi, hakan zai taimaka sosai wajen yaki da rashin tsaro.

An nemi gwamnoni su cika alkawari

Taron ya kuma bayyana amincewarsa da kafa sabon Kwamitin Amintattu na Asusun Tsaro na Arewacin Najeriya, tare da bukatar mambobinsa su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da adalci.

Gwamnonin Arewa.
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal tare da wasu gwamnoni a taron Kaduna Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Mahalarta taron sun yabawa jihohin da suka fara cika alkawarinsu na bayar da Naira biliyan daya duk wata domin tallafawa Asusun Tsaro na Arewa.

Sun kuma bukaci sauran jihohi su rika cika alkawuran da suka dauka ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda Leadership ta kawo.

Sarkin Musulmi ya ba Arewa shawara

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar III ya yi kira ga dukkan 'yan Arewa da su hada kai wajen yakar 'yan bindiga da sauran yan ta'adda.

Sultan ya fadi haka ne a jiya Laraba a taron hadin gwiwa da aka gudanar a birnin Kaduna, inda sarakunan gargajiya da gwamnonin yankin Arewa suka hadu.

Sarkin Musulmi ya bayyana cewa tsaro ya zama aikin dukan al'umma, ba na hukumomi ko gwamnoni koNsarakuna kadai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262