An Saki Sunayen Gwamnoni 5 da Ministoci da Za Su Wakilci Najeriya a Taron Kanada

An Saki Sunayen Gwamnoni 5 da Ministoci da Za Su Wakilci Najeriya a Taron Kanada

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da tawagar gwamnati da za ta wakilci Najeriya a taron zuba jari na farko tsakanin ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje
  • Femi Gbajabiamila ne zai jagoranci tawagar da ta ƙunshi gwamnoni biyar da ministoci da wakilan manyan hukumomin gwamnatin tarayya
  • Wannan babban taron zai mayar da hankali kan noma, fasaha, masana’antu, ababen more rayuwa, makamashi, lafiya da tattalin arzikin dijital

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da wata tawagar gwamnatin tarayya da za ta wakilci Najeriya a taron farko na zuba jari na 'yan Najeriya mazauna waje da za a gudanar a Toronto, Canada.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ne zai jagoranci tawagar zuwa taron da aka sanya wa taken “Invest Nigeria, Thrive Abroad”, wanda zai gudana daga ranar 12 zuwa 15 ga Agusta.

Tinubu ya zabi Femi Gbajabiamila ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron Kanada
Femi Gbajabiamila ya na nunawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu wani abu a cikin takarda. Hoto: Aso Rock Villa
Source: Facebook

An tura gwamnoni taro Kanada

Gwamnonin da za su kasance cikin tawagar sun haɗa da Babagana Zulum na Borno, Chukwuma Soludo na Anambra, Uba Sani na Kaduna, Caleb Mutfwang na Plateau da Dauda Lawal na Zamfara, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Halin da wasu ƴan Najeriya ke ciki a gidan gyaran hali na Saudiyya

Sauran jami’an da za su halarci taron sun haɗa da Ministan Harkokin Waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu, Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Jumoke Oduwole, da Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo.

Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM) ce ta sanar da shirye-shiryen taron cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Juma’a.

Wadanda za su wakilci Najeriya

Sanarwar ta bayyana cewa wakilan Babban Bankin Najeriya, Hukumar Kwastam, Hukumar Shige da Fice, Hukumar Haraji ta Najeriya da Hukumar Inganta Zuba Jari ta Najeriya za su halarta.

Ana kuma sa ran wakilan wasu hukumomi kamar Hukumar Bunƙasa Fitar da Kayayyaki ta Najeriya da Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa za su shiga taron.

Shugabar NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa, ta ce yawan manyan jami’an da za su halarci taron ya nuna ƙudirin Tinubu na ƙarfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin Najeriya da Canada ta fuskar ciniki, zuba jari da hulɗa da ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Jiha 1 a Arewa ta shirya hada mutane miliyan 1 su zabi Tinubu a 2027

Ta bayyana taron a matsayin wani dandali da zai haɗa masu zuba jari na ƙasashen waje da shirye-shiryen zuba jari da suka tanadi komai a muhimman sassan tattalin arzikin Najeriya.

Waɗanne fannoni za a tattauna?

A cewar hukumar NiDCOM, taron zai mayar da hankali kan fannoni da dama da suka haɗa da noma, fasaha, masana’antu, ababen more rayuwa, makamashi, kiwon lafiya da tattalin arzikin dijital.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zabi tawagar da za ta wakilci Najeriya a taron Kanada
Shugaba Bola Ahmed a zauren majalisar zartarwa ta tarayya da ke a fadar shugaban kasa. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Hukumar ta shirya taron ne tare da haɗin gwiwar Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Ottawa, Babban Ofishin Jakadancin Canada da ke Abuja da sauran masu ruwa da tsaki.

Rahoton ya nuna cewa wannan ne karon farko da gwamnatin tarayya, ta hannun NiDCOM, ta shirya wani taron da aka mayar da hankali musamman kan zuba jari da haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin Najeriya da ’yan kasarta da ke ƙasashen waje.

A cewar Bankin Duniya, Najeriya na cikin ƙasashen Afirka da ke karɓar makudan kuɗaɗen da ’yan kasarta ke aikawa daga ƙasashen waje, abin da ke nuna muhimmancin rawar da ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje za su iya takawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.

Kara karanta wannan

Izala ta shirya babban taro na tarihi a Abuja, an gayyaci manyan baki

Saudiyya ta yi wa Tinubu gayyata

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya karɓi gayyata daga Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman domin halartar babban taron zuba jari na FII.

Jakadan Saudiyya a Najeriya ne ya miƙa gayyatar ga shugaban ƙasa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a madadin Yariman Saudiyya.

Tinubu ya yabawa dangantakar Najeriya da Saudiyya, yana mai cewa haɗin gwiwar ƙasashen biyu na ci gaba da ƙarfafa a fannoni daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com