Bashin da Ake Bin Najeriya Ya Hausa Naira Tiriliyan 159, DMO Ta Fayyace Komai

Bashin da Ake Bin Najeriya Ya Hausa Naira Tiriliyan 159, DMO Ta Fayyace Komai

  • Bashin gwamnatin Najeriya ya karu zuwa Naira tiriliyan 159.35 a karshen watan Maris na 2026 bayan karin kusan Naira tiriliyan 10 cikin shekara guda
  • Bayanai sun nuna gwamnatin tarayya ta ci gaba da zama mafi girman mai karbar bashi, yayin da bashin cikin gida ya fi karfi a tsarin bashin kasar
  • Darajar bashin waje a naira ta ragu saboda karfafa darajar naira da aka yi amfani da ita wajen sauya bashin daga dalar Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

FCT, Abuja – Jimillar bashin gwamnatin Najeriya ta kai Naira tiriliyan 159.35 a karshen watan Maris na shekarar 2026.

Jimillar bashin ta kai hakan ne bayan da ta karu da kusan Naira tiriliyan 10 cikin shekara guda, kamar yadda sabbin alkaluman Hukumar Kula da Basussuka (DMO) suka nuna.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Atiku ya shiga damuwa bayan tura kudi masu yawa a asusunsa

Ana bin Najeriya bashi
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Binciken da The Punch ta gudanar kan bayanan DMO ya nuna cewa bashin ya karu da Naira tiriliyan 9.96, wato kashi 6.67 daga Naira tiriliyan 149.39 a karshen watan Maris na 2025 zuwa Naira tiriliyan 159.35 a watan Maris na 2026.

Idan aka auna da dalar Amurka, bashin ya karu da kashi 18.22, inda ya tashi daga dala biliyan 97.24 zuwa dala biliyan 114.95 a cikin wannan lokaci.

Karamin kari tsakanin Disamba da Maris

Sai dai karin bashin tsakanin watan Disambar 2025 da Maris na 2026 bai yi yawa ba idan aka auna da Naira.

Jimillar bashin ta karu da Naira biliyan 75.51 kacal, wato kashi 0.05, daga Naira tiriliyan 159.28 zuwa Naira tiriliyan 159.35.

Amma idan aka auna da dala, bashin ya karu da dala biliyan 3.98, wanda ya kai kashi 3.59, daga dala biliyan 110.97 zuwa dala biliyan 114.95.

Sauyin farashin canjin kudi ya shafi lissafin bashi

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin marigayi Buhari ta kashe N1.16trn na tallafin man fetur

Bambancin da aka samu tsakanin alkaluman Naira da dala ya samo asali ne daga sabon farashin canjin kudin da DMO ta yi amfani da shi wajen mayar da bashin waje zuwa Naira.

Hukumar ta yi amfani da farashin canji na Babban Bankin Najeriya (CBN) na N1,386.2156 kan dala daya a watan Maris na 2026, idan aka kwatanta da N1,435.2571 kan dala daya a karshen watan Disambar 2025.

Hakan ya nuna cewa darajar nairar da aka yi amfani da ita wajen lissafin bashin ta karu da kusan kashi 3.42.

Saboda haka, duk da cewa bashin waje ya dan karu idan aka auna da dala a farkon watanni uku na shekarar 2026, darajarsa ta Naira ta ragu sosai.

Bashin waje ya ragu da naira, bashin cikin gida ya karu

Bashin waje ya tsaya kan dala biliyan 51.90 a watan Maris, bayan karin dala miliyan 48.05 kacal daga dala biliyan 51.86 a watan Disamba.

Sai dai idan aka mayar da shi zuwa Naira, darajarsa ta ragu da Naira tiriliyan 2.48, wato kashi 3.33, daga Naira tiriliyan 74.43 zuwa Naira tiriliyan 71.95.

A gefe guda kuma, bashin cikin gida ya karu da Naira tiriliyan 2.55, wanda ya kai kashi 3.01%, daga Naira tiriliyan 84.85 zuwa Naira tiriliyan 87.40.

Kara karanta wannan

Izala ta shirya babban taro na tarihi a Abuja, an gayyaci manyan baki

Saboda haka, bashin cikin gida ya zama kashi 54.85 na jimillar bashin Najeriya a watan Maris, idan aka kwatanta da kashi 53.27% a watan Disamba. Hakazalika, kaso na bashin waje ya ragu daga kashi 46.73 zuwa kashi 45.15.

Gwamnatin Tinubu ta runtumo basussuka
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Amfanin da gwamnatin Tinubu ke yj da bashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta kare manufar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na karɓo bashi.

Ta bayyana ewa manyan ayyukan more rayuwa da ake gani a jihohin Najeriya sun tabbatar da cewa ana amfani da kuɗin bashin wajen ci gaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com