
Arewa







Rundunar tsaro ta dakile harin ramuwar gayya na ‘yan bindiga a Mada, karamar hukumar Gusau, jihar Zamfara inda ta yi nasarar hallaka hatsabibin dan ta'adda.

Alhaji Attahiru Bafarawa ya musanta shiga SDP, yana mai cewa labaran ba su da tushe. Ya shaida cewa yanzu ya mayar da hankali kan gina rayuwarsa a wajen siyasa.

Gwamnan jihar Jigawa ya kai ziyarar gani da ido kan yadda shirin raba abinci na watan azumin Ramadan ke guduwa. Gwamnan ya nuna damuwa kan abin da ya gani.

Kotun Adamawa ta dage shari’ar da ke kalubalantar kafa Masarautar Fufore. Lauyan masu kara ya nemi karin lokaci don martani ga takardar da gwamnatin jiha ta gabatar.

Gwamnatin jihar Gombe ta karyata zargin shugaban SDP na jihar Gombe da ya ce gwamna Inuwa Yahaya ya nemi ya zabga masa mari a filin jirgin sama da suka hadu.

Wata ƙungiyar matasa a Arewacin Najeriya mai suna 'Young Nigerian Voices' ta bukaci tsohon minista, Hon. Emeka Nwajiuba ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

‘Yan ta’addar Lakurawa sun kashe mutum 13 a Birnin Dede, Kebbi, sun kona kauyuka 7, a ramuwar gayya bayan kisan shugabansu Maigemu da dakarun tsaro suka yi.

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Chief Patrick Adaba, ya rasu yana da shekaru 79 a ranar Lahadi a Abuja, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Gwamnatin Bola Tinubu ta amince da samar da motoci masu aiki da wutar lantarki 10,000 a wasu Arewa maso Gabas. Za a samar da wuraren cajin motocin.
Arewa
Samu kari