Masanin da Ya Yi Tsayuwar Daka Yana Kare Musulunci a Amurka Ya Rasu
- Fitaccen malamin jami'ar Georgetown ya rasu bayan kwashe shekaru da dama yana gina fahimtar juna tsakanin Musulmai da Turai
- Farfesa John Esposito ya wallafa littattafai sama da 50 inda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaki da kyamar Musulunci a duniya
- Shugabannin kasashen Musulmi da dama sun aike da sakwannin ta'aziyya tare da bayyana shi a matsayin babban aminin daular Musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Farfesa John L. Esposito, wanda ake kallo a matsayin ɗaya daga cikin fitattu kuma kwararrun masana da ba Musulmai ba da suka fi tasiri wajen kare martabar Musulunci, ya rigamu gidan gaskiya yana da shekaru 86.
Iyalan malamin da kuma mahukunta na Jami'ar Georgetown da ke Amurka ne suka tabbatar da cewa ya rasu a ranar 15 ga watan Yuli, bayan kwashe sama da shekaru hamsin yana aikin koyarwa da bincike.

Source: Facebook
Al Jazeera ta rahoto cewa Esposito ya sadaukar da rayuwarsa wajen gyara kuskuren fahimta da kasashen Yamma ke da shi game da addinin Musulunci, inda ya samar da hanyoyin tattaunawa ta gari tsakanin Musulmai da sauran al'ummomi.
Asalin karatunsa da gina cibiyoyi
An haife shi a Brooklyn, New York a shekarar 1940, inda ya yi karatu a ƙarƙashin fitaccen masanin nan dan asalin Falasdinu da Amurka, Isma'il Raji al-Faruqi, wanda ya koya masa dabarun gabatar da Musulunci yadda yake.
Bayan kwashe shekaru kusan 20 yana koyarwa a kwalejin Holy Cross, ya koma Jami'ar Georgetown inda a shekarar 1993 ya kafa shahararriyar cibiyar nan ta "Prince Alwaleed bin Talal Center for Muslim-Christian Understanding."
A ƙarƙashin jagorancinsa, wannan cibiyar ta zama ɗaya daga cikin manyan rumbun bincike da tattaunawa tsakanin addinai a duniya, sannan ya kaddamar da shirin "Bridge Initiative" don yaƙi da kyamar Musulunci.

Kara karanta wannan
Matasa sun fito farautar 'yan bindiga bayan kashe wani jagoran al'umma a jihar Katsina
Littattafai da lambobin yabo
Shafin Muslim Matters ya wallafa cewa Esposito ya rubuta da kuma gyara littattafai sama da 50 a lokacin rayuwarsa, waɗanda aka fassara su zuwa harsuna 35 na duniya domin amfanin al'umma daban-daban.
Daga cikin manyan littattafansa akwai Islam: The Straight Path da kuma Who Speaks for Islam? wanda ya rubuta tare da Dalia Mogahed bayan sun tattauna da Musulmai sama da 50,000 a ƙasashe 35.
Saboda gudunmawar da ya bayar, ya taba samun babban lambar yabo ta "Martin E. Marty Award" a Amurka da kuma lambar girma ta "Quaid-e-Azam" daga gwamnatin ƙasar Pakistan.

Source: Facebook
Shugaban ƙasar Malaysia, Anwar Ibrahim, ya nuna alhininsa inda ya bayyana Esposito a matsayin "sahihi kuma amini na gaskiya ga duniyar Musulmi" wanda ya kare Musulunci musamman bayan harin 11 ga Satumba.
Isra'ila ta dakatar malami
A wani rahoton na daban, mahukuntan ƙasar Isra'ila sun dakatar da babban Mufti na birnin Kudus da ƙasar Palasdinu, Sheikh Muhammad Hussein, daga shiga masallacin Al-Aqsa na tsawon mako guda.

Kara karanta wannan
'Yan Arewa za su amfana da Amurka ta kawo tallafi mai kyau a fannoni 3 a Najeriya
Gwamnatin yankin Kudus ta tabbatar da cewa jami'an tsaron Isra'ila sun tsare Sheikh Hussein ne jim kaɗan bayan ya gama gabatar da huɗubar ranar Juma'a a masallacin na Al-Aqsa.
Hukumomin na Isra'ila sun bayyana cewa sun kama shi ne saboda abubuwan da ya faɗa a huɗubarsa, inda ya yi addu'ar neman rahama ga Palasdinawa da Isra'ila ta kashe da kuma neman agaji ga waɗanda ke tsare a gidajen yari.
Asali: Legit.ng
