2027: Babban Jigon APC a Arewa Ya Tada Rigima, Ya Ce Ba Zai Sake Tallata Tinubu ba

2027: Babban Jigon APC a Arewa Ya Tada Rigima, Ya Ce Ba Zai Sake Tallata Tinubu ba

  • Jigon APC a jihar Kebbi, Adamu Yahaya, ya sanar da janye goyon bayansa ga Shugaban kasa, Bola Tinubu gabanin zaben 2027
  • Ya ce ya shafe sama da shekara biyu yana tallata ayyukan gwamnatin Tinubu da kudinsa ba tare da samun kulawa ba
  • Ya bayyana cewa ba zai ci gaba da yada shirye-shiryen gwamnatin tarayya ba saboda rashin nuna masa muhimmanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kebbi, Nigeria - Yayin da ake tunkarar zaben 2027, wani jigon jam'iyyar APC a jihar Kebbi, Adamu Yahaya, wanda aka fi sani da Adam Fakai, ya sanar da janye goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Fakai ya ce ya dauki wannan mataki ne saboda abin da ya bayyana a matsayin rashin hada kai da kuma rashin samun kulawa daga shugabannin jam'iyyar, duk da irin gudummawar da ya ce ya bayar.

Kara karanta wannan

'Babu kamar shi': An fadi bangaren da Tinubu ya fi sauran shugabannin Najeriya

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yaka jawabi a wurin taro Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Dalilin jigon APC na juyawa Tinubu baya

Rahoton Leadershirp ya ce a wata sanarwa da ya fitar, Fakai ya ce ya shafe sama da shekara biyu yana amfani da kudinsa, lokacinsa da karfinsa wajen yada ayyuka da manufofin gwamnatin Tinubu a fadin Arewa da Kudu.

Ya ce ya yi hakan ne saboda ya yi imani cewa gwamnatin Tinubu za ta kawo ci gaba a fadin Najeriya.

Cakai ya ce:

"Na shafe sama da shekara biyu ina amfani da kudina, lokacina da karfina wajen tallata shirye-shirye da nasarorin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga 'yan Najeriya a Arewa da Kudu."

Ya koka kan rashin kulawa daga APC

Fakai ya ce duk da irin kokarin da ya yi, bai samu wata irin godiya, karfafa gwiwa ko tallafi daga shugabannin APC a jihar Kebbi ko a matakin tarayya ba.

Ya kuma yi zargin cewa wasu manyan 'yan siyasa na amfani da hotuna da bidiyoyin ayyukan gwamnati da ya dauka ba tare da tuntubarsa ko nuna masa godiya ba.

Kara karanta wannan

"Na ji kunya": Tinubu ya ba EFCC umarnin bude asusun gwamnatin Osun da aka rufe

Ya dakatar da tallata gwamnatin Tinubu

Fakai ya bayyana cewa saboda wannan hali da ake nuna masa, ya yanke shawarar dakatar da duk wani yunkuri na tallata ayyuka da manufofin gwamnatin Shugaba Tinubu.

Sai dai ya gode wa mutanen da suka kasance suna karfafa masa gwiwa da addu'o'i a lokacin da yake gudanar da wannan aiki.

Tutar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Getty Images

An san Adam Fakai a kafafen sada zumunta saboda yadda yake kai ziyara zuwa manyan ayyukan gwamnatin tarayya tare da wallafa hotuna, bidiyoyi da rahotanni domin sanar da jama'a irin ayyukan da ake aiwatarwa.

Dalilin da zai Tinubu ya lashe zaben 2027

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Orji Kalu, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba shi da wata babbar barazana daga 'yan adawa kafin zaɓen 2027.

Ya ce jam'iyyun adawa sun yi rauni matuƙa saboda sun gaza haɗuwa a ƙarƙashin tsari guda da kuma tsayar da ɗan takara ɗaya.

Kalu ya ƙara da cewa Tinubu yana da "maƙiya da dama" a cikin gwamnati da kuma wajen gwamnati waɗanda ke aiki domin kawo cikas ga tafiyar mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262