Gwamnatin Kano Ta yi Kuskuren Tura wa Wani Mutum Kudin Fanshon Miliyoyi
- Gwamnatin jihar Kano ta yi kokarin aika wa wani ma’aikaci kudin sallamarsa sai aka samu babban kuskure
- Yanzu haka kudin sun shige cikin asusun wani mutumi dabam da yake jihar Neja a Arewa maso tsakiya
- Wannan bawan Allah mai amana ya sanar da duniya cewa an samu tuntube, ya bukaci a raba shi da kudin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - A ‘yan kwanakin nan ne Gwamnatin jihar Kano ta yi wani kuskure da ya nuna amana da gaskiyar wani bawan Allah.
A kokarin tura kudin giratuti na wani ma’aikaci, sai gwamnati ta samu tuntube ta aika wannan kudi zuwa wani mutum dabam.

Source: Facebook
Kuskuren aika wa wani mutumi giratuti
Ja’afar Ja’afar a shafinsa na Facebook ya bayyana yadda N5.3m suka shiga cikin asusun bankin wannan mutum mai gaskiya.

Kara karanta wannan
Dalilin Atiku na jawo Amaechi su yi takarar shugaban kasa tare a ADC ya fito fili
Miliyoyin kudin suna shigo masa sai ya fara kokarin ganin yadda za a maida wa wanda ya aiko su, amma abin bai yiwu ba.
Ganin haka ne sai ya tuntubi babban ‘dan jaridar ya taimaka masa wajen ganin an raba shi da dukiyar da bai cancance ta ba.
‘Dan jaridar ya rubuta:
“Gwamnatin Kano ta yi kuskuren aika girtatutin N5.3m ga wanda ba shi aka nufa da kudin ba.
Gaskiyar wannan bawan Allah ta fito karara
Saboda tsabagen gaskiya, wanda aka yi kuskuren aika wa kudin ya yi maza ya tuntubi bankin shi domin a maida kudin.
Sai dai bankin ba su iya maida kudin inda suka fito ba. Yanzu ya tuntube ni yana neman yadda kudin za su koma wa asalin mai hakkinsu.
A karshe Malam Ja’afar Ja’afar ya kare da cewa: “Na Allah ba sa ƙarewa!”
Da ya tuntubi shugaban gidan jaridar na Daily Nigerian, sai ya fada masa sunansa, yana neman a sanar da ma’aikatar gwamnati.
Yadda ya tuntubi Ja'afar Ja'afar a Facebook
Ya ce:
"Assalamu Alaikum, Malam Ja’afar, sunana XXXXXXXXXXXXX (an boye suna), an yi kuskuren aiko mani kudi ne daga gwamnatin jihar Kano.
"Na kira banki na, na fada masu amma har yanzu ba a maida kudin ba. A taimaka a fada wa ma’aikatar da abin ya shafa wannan kuskure da aka yi."
- Inji mutumin
Hotunan da aka wallafa sun nuna a lokacin da wannan kudi har N5.3m suka shigo masa, N29 kacal ne a cikin asusun bankin nasa.
An tura kudin ne cikin asusun da ke bankin Ja’iz a Neja a lokacin da aka nufi wani ma’aikaci da ya gama yi wa jihar Kano aiki.
Kudin wasu mahajjatan 1447 zai dawo
Bayan an gama aikin hajji, sai ga labari cewa kudin wasu alhazan Najeriya zai dawo inji shugaban hukumar NAHCON na kasa.
Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta yi albishir da shirin mayar wa mahajjata wasu daga cikin kudin da suka biya.
Wannan zai shafi mahajjatan da suka biya wani kudin aiki da ba a yi masu ba, ko kamfanonin Saudin ba su sauke nauyin da kyau ba.
Asali: Legit.ng
