'Yan Bindiga Sun Tafka Barna a Sokoto, Sun Kashe Basarake, Ɗansa da Wasu Mutane

'Yan Bindiga Sun Tafka Barna a Sokoto, Sun Kashe Basarake, Ɗansa da Wasu Mutane

  • 'Yan bindiga sun kashe Maigarin Kulodo, babban ɗansa da wasu mutane a hare-haren da suka kai ƙauyukan ƙaramar hukumar Bodinga a Sakoto
  • Maharan sun yi awon gaba da dimbin dabbobi zuwa wani daji a Zamfara, yayin da mata da yara suka tsere daga ƙauyukan saboda fargabar harin
  • Daruruwan matasa sun tare babbar hanyar Sokoto zuwa Jega domin nuna adawa da yawaitar hare-haren da suka tilasta wa mutane barin gidajensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Sokoto – Wasu 'yan bindiga sun kashe Maigarin Kulodo da ke ƙaramar hukumar Bodinga a jihar Sokoto, Alhaji Abubakar Tudu, tare da babban ɗansa da wasu mutum huɗu a wani sabon hari da suka kai yankin.

Maharan sun kuma kashe wani mutum guda a ƙauyen Kwance da ke makwabtaka da Kulodo, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin al'ummar yankin.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun bindige yaro dan shekara 10, sun sace matan aure a Sokoto

'Yan bindiga sun kashe Maigari, dansa da wasu mutane a Kano
Wata mata zaune a kusa da kangon gidanta a kauyen Kawuri, jihar Borno bayan harin Boko Haram da ya yi ajalin mutum 70. Hoto: STRINGER / Getty Images
Source: Getty Images

An kashe maigari, dansa da mutane 5

Harin ya faru ne da misalin lokacin sallar La'asar, inda maharan suka mamaye ƙauyukan biyu da babura suna harbe-harbe kan mai uwa da wabi, in ji rahoton Daily Trust.

Wata majiya ta tsaro ta shaida wa manema labarai cewa maharan sun shiga Kulodo da Kwance da yawa, inda suka fara bude wuta kan mazauna yankin.

Mutanen da aka kashe a Kulodo sun haɗa da Maigari Alhaji Abubakar Tudu, babban ɗansa Abubakar Abubakar, Rufa'i Bala, Muhammad Sanusi da Aliyu Dan-Uti.

A ƙauyen Kwance kuwa, an kashe wani mutumi mai suna Yellow Dikko.

Majiyar ta ce:

"Sun shiga ƙauyukan da yawa kuma suka fara harbe-harbe. Sun kashe shugaban ƙauyen, babban ɗansa da wasu mutum huɗu kafin su wuce ƙauyen Kwance inda suka kashe wani mutum."

Maharan sun sace dabbobi zuwa dajin Zamfara

Rahotanni sun nuna cewa maharan ba su yi garkuwa da kowa ba, sai dai sun yi awon gaba da dumbin shanu da sauran dabbobi.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Sojoji sun rike masu kera makamai ga 'yan ta'addan Arewa ta yamma

An ce sun tilasta wa makiyaya su kora musu dabbobin zuwa wani daji a jihar Zamfara kafin daga bisani suka sake su su koma gida.

Majiyar ta bayyana cewa:'

"Babban abin da suka zo nema shi ne dabbobi. Sun sa makiyaya suka kora musu shanun zuwa cikin daji a Zamfara kafin daga baya suka sake su."
Matasa sun yi zanga zanga a Sokoto kan hare-haren 'yan bindiga.
Taswirar jihar Sokoto, inda 'yan bindiga suka kashe Maigari da mutane 6. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mata da yara sun tsere daga ƙauyukan

Bayan harin, mafi yawan mata da yara sun tsere daga Kulodo da Kwance saboda fargabar sake kai hari.

Majiyar ta ce tawagar jami'an gwamnatin jihar da wasu 'yan majalisa sun kai ziyarar jaje yankin, inda suka tarar da ƙauyukan sun kusa zama kufai.

A ranar Juma'a kuma, daruruwan matasa sun tare babbar hanyar Sokoto zuwa Jega domin nuna rashin jin daɗinsu kan yawaitar hare-haren 'yan bindiga a ƙaramar hukumar Bodinga.

Masu zanga-zangar sun kunna tayoyi a kan hanya, lamarin da ya dakatar da zirga-zirga na sa'o'i kafin jami'an tsaro suka tarwatsa su.

'Yan bindiga sun kashe limami a Sokoto

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun sake kai hare-hare a wasu kauyukan jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa masu koyon karatun Alkur'ani wuta a Bauchi

Hatsabiban 'yan bindigan sun hallaka wani babban limami tare da wasu mutane a hare-haren wadanda suka kai a kauyuka biyu.

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigan sun kuma yi awon gaba da dabbobi masu dumbin yawa yayin hare-haren da suka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com