'Yan Bindiga Sun Tare Matafiya, Sun Budewa Jama'a Wuta
- Wasu 'yan bindiga sun bude wa motar kasuwa wuta a hanyar Mokwa–Kainji, sannan sun jefa jama'a a cikin tashin hankali da fargaba
- Mazauna sun ce hare-haren sun koma ruwan dare a hanyar, lamarin da ke jefa matafiya cikin hadari da tsoron tafiya da wucewa ta hanyar
- An ce a ranar Talata 4 ga watan Yuli, 2026 ma 'yan bindigar sun kashe mutum hudu tare da yin garkuwa da wasu da dama a wannan hanya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger – Wani mazaunin yankin mai suna Aliyu Alhassan ya bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun bude wa wata motar kasuwa wuta bayan sun yi mata kwanton bauna a kan hanya
Wannan lamarin da ya sa fasinjoji biyu suka samu raunukan harbin bindiga yayin da aka rika gudun neman tsira domin samun mafaka.

Source: Original
A hirar da Aliyu Alhassan ya yi da jaridar Aminiya, ya ce an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa wani asibiti da ke kusa domin ba su kulawa.
An kai hari kan matafiya Neja
Aliyu Alhassan ya kara da cewa da yawa daga cikin matafiyan sun makale a hanya yayin da yan bindiga ke ci gaba da neman mafaka.

Source: Twitter
A cewarsa:
"Harin ya sa direbobi da sauran matafiya da dama suka makale a hanya. A jiya (Talata) ma 'yan bindiga sun tare wannan hanyar ta Mokwa zuwa New Bussa, inda suka kashe mutum hudu tare da yin garkuwa da wasu da dama."
Aliyu ya kuma bayyana cewa yawaitar irin wadannan hare-hare ta mayar da hanyar Mokwa–Kainji daya daga cikin wuraren da matsalar tsaro ta fi kamari, inda ake samun hare-hare kusan kullum.
Abin da yan sandan Neja suka ce
Da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, domin jin ta bakin rundunar, bai samu damar yin karin bayani ba.
Ya shaida wa Legit cewa:
"Na yi kokarin ji tuntubar yan sandanmu da ke wannan yankin, amma ban samu su ba sabooda matsalar 'network', da zarar na same su, zan sanar da ku."
Wannan al'amari ya kara ta'azzara matsalar tsaro da ake fama da shi a Arewa maso Yammacin kasar nan wanda ya hada da matsalar yan bindiga masu garkuwa da mutane da hana zaman lafiya a yankin.
An kai hari jihar Neja
A baya, mun wallafa cewa rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun sace dagacin ƙauyen Patiko, Mallam Haruna Abubakar, a gundumar Zugurma da ke karamar hukumar Mashegu a jihar Neja.
Wani mazaunin yankin mai suna Aliyu Usman ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun mamaye ƙauyen ne da tsakar daren ranar Juma’a, 31 ga watan Yulin 2026 wanda ya jefa jama'a a cikin wahala.
A cewar Aliyu Usman, ‘yan bindigar sun kira wasu mutane ranar Asabar, 1 ga watan Agustan 2026 inda suka nemi a biya Naira miliyan 80 kafin a sako dagacin lamarin da har yanzu ke hana jama'a kwanciyar hankali.
Asali: Legit.ng

