'Sai Arewa Ta Yi Tsayin Daka': Inuwa Yahaya Ya Zaburar da Gwamnoni Kaduna
- Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da sakatariyar wucin gadi tna shiyyar a jihar Kaduna
- Da ya ke jawabi, Muhammad Inuwa Yahaya wanda shi ne gwamnan jihar Gombe ya bayyana burin da shiyyar Arewa ke da shi domin a samar da ci gaba
- Gwamnonin Arewa sun jaddada aniyarsu ta ƙarfafa haɗin gwiwa domin magance matsalolin tsaro, tattalin arziki da ci gaban yankin da a yanzu ke cikin wani hali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewacin Najeriya (NNGF) kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da sakatariyar wucin gadi ta ƙungiyar a Kaduna.
An buɗe sakatariyar ne a gini mai lamba 26 da ke kan titin Muhammadu Buhari , tare da miƙa motocin aiki domin sauƙaƙa gudanar da ayyukan ƙungiyar.

Source: Facebook
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a 10 ga watan Yuli, 2026.
Gwamnonin Arewa sun zauna a Kaduna
A cewarsa, kafa sakatariyar wata muhimmiyar alama ce ta sabon mataki da ƙungiyar ta shiga wajen ƙarfafa ayyukanta da kuma samar da mafita ga matsalolin tattalin arziki, zamantakewa da tsaro da yankin Arewa ke fuskanta.
Muhammad Inuwa Yahaya ya bayyana cewa sabon ofishin zai taimaka wajen daidaita manufofi, shirye-shirye da haɗin gwiwa tsakanin jihohin Arewa 19.

Source: Facebook
Gwamnan jihar Gombe ya kuma buƙaci gwamnonin Arewa da sauran shugabannin yankin su ci gaba da haɗa kai domin fuskantar ƙalubalen da ake ciki.
Ya ce:
"Ya kamata abubuwan dake faruwa su jagorance mu wajen magance ƙalubalen da Arewa ke fuskanta a yau. Irin waɗannan gine-gine shugabanninmu na farko ne suka yi su shekaru da dama da suka gabata. Me zai hana mu ɗora a kan harsashin da suka kafa? Dole ne mu jajirce kan nagarta, mu ci gaba da mai da hankali, don bar wa yan baya kyakkyawan tarihi."
Gwamna ya zaburar da Arewa
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya ƙara da cewa halin da Arewa ke ciki yanzu na buƙatar ƙarin sadaukarwa da matakan haɗin gwiwa, yana mai cewa taswirar da ƙungiyar ta tsara za ta taimaka wajen cimma burin ci gaban yankin.
Ya ce:
"Yanayin da ake ciki a Arewacin Najeriya yana buƙatar mu ƙara ɗaukar matakai don magance yanayin da muka tsinci kanmu a ciki. Ina ganin cewa da taswirar da muka shimfida, zamu iya cimma duk abin da muke buƙata. Cimma burinmu na haɗin gwiwa yana buƙatar sadaukarwa da jajircewar kowannenmu."
A nasa jawabin, gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris, ya ce gwamnonin Arewa za su ci gaba da ƙarfafa haɗin kai domin tinkarar matsalolin yankin.
Ya yabawa Inuwa Yahaya kan jagorancinsa, yana mai cewa kafa sakatariyar ta nuna sabon ci gaba ga ƙungiyar, wadda ta shafe shekaru tana gudanar da ayyukanta ba tare da cikakkiyar sakatariya ba.
Gwamnonin Arewa sun taru a Kaduna
A wani labarin, kun ji cewa gwamnonin jihohin Arewa 19 da sarakuna sun amince da kara hadin gwiwa wajen magance matsalar tsaro da ta addabi yankinsu kama daga rashin tsaro da matsalar tattalin arziki.
A taron da suka gudanar a Kaduna, sun yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen yaki da rashin tsaro, wanda har yanzu wasu sassan jihohin shiyyar ke fama da rashin kwanciyar hankali.
Gwamnoni da sarakunan Arewa sun kuma tabbatar da cikakken goyon bayansu ga shirin kafa 'yan sandan jihohi domin inganta tsaro, ganin yadda zai ba gwamnonin karin iko wajen tabbatar da tsaro a jihohinsu.
Asali: Legit.ng


