2027: Sabon Rikici Ya Bulla a Kano tsakanin APC da Dan Bilki Kwamanda

2027: Sabon Rikici Ya Bulla a Kano tsakanin APC da Dan Bilki Kwamanda

  • Danbilki Kwamanda ya yi watsi da sanarwar da shugabannin APC na Kano suka yi kan dakatar da shi daga jam’iyyar, yana mai cewa babu wanda ya isa ya kore shi
  • Kwamanda ya ce ya shiga APC ne da ra’ayinsa kuma ba ya tsoron fuskantar abokan hamayyarsa, yana mai cewa zai cigaba da fadin ra’ayinsa kan abubuwan da suka shafi jam'iyyar
  • Ya kuma caccaki shugabannin APC na Kano kan abin da ya kira rashin mayar da hankali kan matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar da nema mata mafita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano – Jigo a jam’iyyar APC a Kano, Abdulmajeed Danbilki Kwamanda, ya yi watsi da sanarwar shugabannin jam’iyyar ta jihar da ta ce an dakatar da shi daga jam’iyyar.

Kwamanda ya ce bai amince da matakin ba, yana mai cewa babu wani mutum ko rukunin jama'a da yake da ikon korarsa daga APC.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya fadi babban abin da yake so a rika tuna shi bayan barin mulki

Abdulmajid Danbilki Kwamanda
Danbilki Kwamanda da ya ce ba zai bar APC ba. Hoto: Abdulmajid Almustapha Kwamanda
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Facebook, inda ya bukaci shugabannin jam’iyyar APC na Kano su mayar da hankali wajen gina jam’iyyar da warware matsalolin cikinta maimakon mayar da hankali kan batun dakatar da shi.

Maganar korar Dan Bilki a APC

Kwamanda ya ce idan shugabannin jam’iyyar ba su san tsarin da doka ta tanada wajen dakatarwa ko korar ɗan jam’iyya ba, ya kamata su tuntubi wadanda suka taɓa shugabancin jam’iyyar domin su koya musu yadda ake gudanar da irin wannan lamari.

Ya ce:

“Abin takaici ne ace kun fito da sanarwar wai kun dakatar da Abdulmajeed Danbilki Kwamanda daga jam’iyya. Wataƙila kuna tunanin zan yi shiru ko in sauya matsaya. Ku sani, ba haka nake ba.
“Ni bana tsoron kowane abokin hamayyar siyasa. Ina fuskantarsa kai tsaye, ko wanene shi. Kuma wallahi, babu wanda ya isa ya kore ni daga jam’iyyar APC.”

Kara karanta wannan

2027: Babban jigon APC a Arewa ya tada rigima, ya ce ba zai sake tallata Tinubu ba

Ya cigaba da bayyana ra’ayinsa

Dan Bilki Kwamanda ya ce kasancewarsa ɗan jam’iyya ba yana nufin ba zai bayyana ra’ayinsa kan abubuwan da yake ganin ba su dace ba.

Ya ce ya shiga APC da ra’ayinsa, ba tare da wani mutum a cikin jam’iyyar ya mallaki ikirarin cewa shi ne ya kawo shi ba.

Ya ce:

“Ra’ayin da na ga ya dace zan bayyana shi a cikin jam’iyya, domin ni ba yaron kowa ba ne a siyasa. Na shiga APC da ra’ayina, kuma babu wani a cikinku da zai ce shi ne ya kawo ni jam’iyyar.”

Kwamanda ya caccaki APC

Kwamanda ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda shugabannin jam’iyyar suka mayar da hankali kan batun dakatar da shi maimakon, a cewarsa, su nemo hanyoyin magance matsalolin da ke addabar APC a Kano.

Ya ce ba neman muƙami ne ya kawo shi siyasa ba, yana mai cewa akida ce ta kawo shi.

Kara karanta wannan

Yadda za ku duba sunayen waɗanda hukumar Kwastam ta ɗauka aiki a 2026

“Ni ba mai neman muƙami ba ne; aƙida ce ta kawo ni siyasa. Duk wani abu da zai cutar da talaka, ba zan goyi bayansa ba.
Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa
Abba Kabir Yusuf na gaisawa da Sule Garo. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa sakataren Yaɗa Labarai na APC na Jihar Kano, Auwal Soja Sani Mainagge, ne ya bayyana hakan yayin da yake magana kan wasu abubuwan siyasa da ke faruwa a jihar.

Dan Bilki ya wallafa sakonnin d ake nuna cewa talakawa na shan azaba a karkashin APC kuma akwai alamun Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sha kaye a 2027.

Imumolen ya janye takara

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na wani ɓangare na jam’iyyar Accord, Farfesa Christopher Imumolen, ya janye wa Bola Tinubu.

Imumolen ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntubar shugabannin ɓangaren jam’iyyarsa, yana mai cewa buƙatar haɗin kan Najeriya.

Ya bayyana janyewarsa a matsayin sadaukarwa ta kishin ƙasa domin fifita ci gaban Najeriya da muradun ƙasa gaba da burin siyasa na kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng