An Yi Kicibis, Sojoji Sun Yi Ram da 'Dan Bindiga a Hanyar Sintiri

An Yi Kicibis, Sojoji Sun Yi Ram da 'Dan Bindiga a Hanyar Sintiri

  • Dakarun rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar kama wani da ake zargin ɗan bindiga a ƙaramar hukumar Danmusa ta jihar Katsina
  • An gano alamun cewa yana ta'ammali da ta'addanci a wani kwarya-kwaryan bincike da aka gundanar a kan wayarsa inda aka gano hujjoji
  • Bayan an damke shi, jaruman sojoji sun kwato babur, wayoyin hannu, katin ATM, katin shaidar ɗan ƙasa da tsabar kudi daga hannunsa nan take

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Rahotanni sun nuna cewa an kama wanda ake zargin mai suna Lawal Sani da misalin a ranar 15 ga Yuli, 2026 lokacin da sojoji ke dawowa daga wani samame da suka kai a yankin Bakori na jihar Katsina.

An ce sojojin sun tsaya na ɗan lokaci a garin Yantumaki, inda suka ci karo da mutumin da suka ga alamun mai laifi ne, suka kuma fara gudanar da bincike a kansa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun rikata 'yan Boko Haram a kananan hukumomin Borno 5

Sojoji sun ci karo da wanda ake zargi da harkokin yan bindiga
Wasu sojojin Najeriya a cikin daji suna aiki Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa majiyoyin tsaro sun bayyana cewa yayin binciken wayar salularsa, an gano wani bidiyo da ake zargin ya nuna Lawal Sani ɗauke da bindigar AK-47.

Sojoji sun kwato kayan 'dan bindiga

Rahoton ya ce bayan gano bidiyon, mutumin ya yi yunƙurin tserewa daga wurin, amma dakarun sojin sun yi gaggawar cafke shi tare da hana shi tserewa.

Sojoji na zurfafa bincike a kan dan bindiga
Taswirar jihar Katsina mai fama da matsalar yan bindiga Hoto; Legit.ng
Source: Original

Bayan kama wanda ake zargin, sojojin sun ce sun kwato wasu kayayyaki da suka haɗa da babur guda ɗaya, wayar Infinix guda ɗaya da wayar Tecno guda ɗaya.

Sauran abubuwan da aka samu sun haɗa da kwafin katin shaidar ɗan ƙasa (NIN), katin ATM na Moniepoint, layin MTN guda ɗaya da kuma kuɗi har N5,020.

Ana ci gaba da binciken dan bindiga

Rahoton ya ce jami'an tsaro sun ci gaba da tsare wanda ake zargin domin zurfafa bincike kan zarge-zargen da ake masa don samun karin hujjoji da bayanan sirri.

Kara karanta wannan

Matasa sun fito farautar 'yan bindiga bayan kashe wani jagoran al'umma a jihar Katsina

Ana sa ran bayan kammala binciken, za a ɗauki matakin shari'a idan aka samu hujjojin da suka dace wadanda za su tabbatar da zargin da su ke yi.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba. Sai dai rahotannin tsaro sun nuna cewa dakarun na ci gaba da gudanar da ayyukan sintiri da farmaki a sassan jihar Katsina.

Jihar Katsina na daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar hare-haren 'yan bindiga a wasu ƙananan hukumomi, lamarin da ya sa jami'an tsaro ke ƙara kaimi wajen gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro.

Sojoji sun samu nasara a Katsina

A baya, mun wallafa cewa rundunar sojojin Najeriya tare da sauran jami'an tsaro sun yi nasarar hallaka 'yan ta'adda takwas a jihar Katsina wadanda suka addabi mazauna yankin da kewaye.

Sojojin sun kai farmakin ne bayan samun sahihan bayanan sirri cewa mabiyan shugaban 'yan ta'adda Idi Abasu Aiki na shirin tare hanya domin kai hari a kan bayin Allah da ke kokarin bi ta wurin.

Rundunar soji ta tabbatar da ƙara sintiri da mamaye yankunan da abin ya shafa, tare da jaddada cewa kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin al'umma yana nan daram duk da kalubalen da ake fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng