Hanyoyi 3 da za a Bi domin Farfado da Arewa cikin Shekaru Kadan

Hanyoyi 3 da za a Bi domin Farfado da Arewa cikin Shekaru Kadan

Yayin da ake cigaba da kokawa kan matsalolin da suka addabi yankunan Najeriya, Dr Usman Bugaje ya fadi hanyoyi uku da za a bi wajen farfado da darajar Arewa a duniya cikin 'yan shekaru.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Daya daga cikin dattawan Arewa kuma tsohon dan majalisar wakilai, Dr Usman Bugaje ya yi magana kan matsalolin da Arewa ke ciki.

Dr Bugaje ya tabbatar da cewa duk da tarin matsalolin da ake fama da su, shawo kansu da daura Arewa a kan turba ba zai dauki lokaci mai tsawo ba.

Arewa House da ke Kaduna
Kofar shiga Arewa House da ke jami'ar ABU. Hoto: Arewa House, Ahmadu Bello University, Zaria
Source: Facebook

Legit ta tattaro galibin abubuwan da Dr Bugaje ya fada ne a wani bidiyo da aka wallafa a shafin A Wata Mahangar a kafar Facebook.

Maganar farfado da Arewa

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi yadda Kiristoci suka karbi tikitin Muslim Muslim a Najeriya

Dr Bugaje ya bayyana cewa yana da kyau a koma baya a kalli darajar da Arewa ta ke da shi, a duba inda aka samu matsala kafin a fara maganar gyara.

Duk da bai bayyana yadda Arewa ta kasance a baya ba, malamin ya yi bayani game da halin da Arewacin Najeriya ke ciki a yau.

Dattajon Arewa, Dr Usman Bugaje
Dr Usman Bugaje yana magana a wajen taro. Hoto: Dr Usman Bugaje
Source: Facebook

Ya bayyana cewa Arewa ce ta fi kowane yanki talauci da jahilci saboda galibin 'yan Arewa, duk da Musulmai ne, sun jahilci addinin Musulunci.

Ya kara da cewa idan aka lura da abubuwan da ake rayuwa da su kamar lantarki, hanyoyi, intanet, ruwan sha da sauransu, Arewa ce koma baya.

Gwamnonin Arewa yayin wani taro
Lokacin da gwamnonin Arewa suka yi taro. Hoto: Abdul No Shaking
Source: Facebook

A kan haka ya bayyana cewa idan aka lura da abubuwan nan, za a tabbatar da cewa Arewa ta zama kurar baya, wanda ba haka ba ne a shekara 50 ko 60 da suka gabata.

Kafin bayyana abubuwan da za a yi amfani da su wajen warware matsalolin, Dr Usman Bugaje ya ce za a iya dunkule cewa babbar matsalar Arewa ita ce shugabanci.

Hanyoyin magance matsalolin Arewa

Yayin da ya ke magana a kan hanyar warware matsalolin Arewa, Dr Bugaje ya ce idan aka samu shugabanci na gare ya fuskanci manyan abubuwa guda uku, Arewa za ta farfado cikin shekara biyar zuwa bakwai.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: 'Dalilin da tikitin Obi,Kwankwaso ya zama mafitar Najeriya '

Ya bayyana cewa abubuwan da zai fada ya gano su ne bayan nazari da bincike kan yadda kasashe ke farfadowa bayan sun kasance cikin rudani.

1. Inganta harkokin noma

Abu na farko da Dr Bugaje ya ambata game da Arewa shi ne habaka noma, saboda, a cewarsa babu wani abu da za a yi a ciyar da alumma gaba idan babu abinci mai gina jiki.

Malamin ya yi tambihi da cewa idan ana maganar noma babu zancen raba taki da 'yan siyasa suke yi, saboda galibi rabon da ake yi na karya ne.

Ya bayyana cewa inda ake abubuwa da gaske, ba a ba mutum taki har sai an san yanayin kasar da ya ke noma, ba kamar yadda ake yi a Najeriya ba.

Wasu manoma na aiki a gona
Wasu mutane a kan hanyar zuwa gona. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya ce farfado da noma ya kunshi samar da hanyoyin noma na zamani da aka yi a irin kasashen Kenya da Rwanda ta yadda manomi ba zai yi hassara ba, idan aka samu matsala kuma, gwamnati za ta shigo ciki.

Daga cikin hanyar inganta noma, malamin ya ce akwai bukatar dakatar da yadda manoma ke sayar da amfaninsu daga gona, ya ce ya dace a samar da hanyar inganta kayan gona kafin sayar da su.

Kara karanta wannan

Kasa ta rikice, mawaki Davido ya fadi yawan miliyoyin da yake kashewa a wata

Ya bukaci a yi tsarin da zai ba manoma damar kai kayan amfaninsu zuwa kasuwannin da ake bukatarsu domin sayar da su da daraja.

2. Inganta harkokin sufuri

A mataki na biyu, Dr Bugaje ya bayyana cewa hanyar da za a bi wajen habaka Arewa ita ce inganta sufuri musamman layin dogo.

Ya bayyana cewa idan aka yi layin dogo daga Arewacin Najeriya zuwa Sudan da Dakar, hakan zai habaka tattalin arzikin Arewa.

Ya bayyana cewa idan mutum yana son kai haja kasashe misali kamar China, ya ce cikin kwana biyu zai isa Sudan wanda kafin wanda yabi Legas ya isa wajen, shi har ya kai kaya zuwa China.

Jirgin kasa na tafiya a titi
Yadda jirgin kasa ke tafiya a Najeriya. Hoto: NRC
Source: Facebook

Malamin ya bayyana cewa idan aka yi haka, Legas da sauran jihohin Najeriya za su dawo zuwa sayen kaya a Kano, saboda saukin harkar sufuri kuma zai fi saukin kudi.

Ya kara da cewa China da bankin cigaban Afrika (AfDB) duk sun yarda za su yi aikin, Najeriya ce kawai ta ki yarda tun lokacin Muhammadu Buhari.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ta ce an yi nisa sosai da aikin layin dogon Kano zuwa Maradi da aka fara a lokacin Buhari.

Kara karanta wannan

An ba da tallafin buta da sauransu a Filato, za a taho Gombe, Kaduna

3. Inganta harkar Intanet

Malamin ya bayyana cewa harkokin intanet kamar fasahar AI ne za su mamaye duniya a shekaru 50 masu zuwa, saboda haka ya ce ya zama wajibi a fara koyawa yara tun daga firamare.

Ya ce duk yadda ake ganin harkokin fasahar zamani yana da wahala, yana da sauki ga duk wanda ya haddace Al-Kur'ani mai girma.

A karshe, Dr Bugaje ya bayyana cewa idan ana maganar fara gyara, dole malamai su dawo cikin hankalinsu, su daina karbar kudi, abinci ko kujerun hajji da Umara wajen 'yan siyasa, su dawo suna fada masu gaskiya.

Malaman addini a Najeriya
Malaman addini da Sultan ya yi zama da su a Kaduna. Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Facebook

Ya kara da cewa ya kamata malamai su dawo alakanta wa'azin da ake yi da abubuwan da suke faruwa domin a rika lalumo hanyoyin magance su.

Daga nan ya ce idan aka samu shugabanni masu tsoron Allah da al'ummar da ba za ta fifita karbar kudi da abubuwa kadan a lokacin zabe da sauransu ba, za a iya samun cigaba.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan ta'adda suka lakadawa dalibai da malaman Oyo duka a daji

Matsayar manyan Arewa kan tsaro

A wani rahoton, mun kawo muku cewa shugabannin Arewa sun yi zama na musamman game da matsalolin da suka addabi yankin a jihar Kaduna.

Gwamnonin jihohi 19 da sarakunan gargajiya sun bayyana cewa samar da 'yan sandan jihohi zai taimaka wajen shawo kan matsalar tsaro a Arewa.

Arewacin Najeriya ta shafe shekaru da dama tana fama da matsalolin tsaro da suka hada da 'yan Boko Haram, 'yan bindiga da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng