An Maka Rarara a Kotu, ana Nema Ya Ba Sheikh Pantami Naira Biliyan 100
- Wani lauya, Sirajo Abubakar, ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Jihar Kano kan Dauda Kahutu Rarara da Adamu Fasaha bisa zargin cin mutuncin Sheikh Isa Ali Pantami
- Mai ƙarar na neman kotu ta hana waɗanda ake ƙarar ci gaba da wallafa ko yaɗa waƙoƙi da wasu abubuwa da ke danganta Pantami da shan miyagun ƙwayoyi da sauransu
- Ƙarar ta kuma nemi a biya Sheikh Pantami Naira biliyan 100 a matsayin diyya, tare da neman a ba shi hakuri da janye abubuwan da aka wallafa a kan sa a cikin wakar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – Wani lauya mai suna Sirajo Abubakar ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Jihar Kano, inda yake neman a kare mutuncin Sheikh Isa Ali Pantami, tare da neman a biya shi N100bn a matsayin diyya.
An shigar da ƙarar ne kan shahararren mawaƙin siyasa na Hausa, Dauda Kahutu Rarara, da wani mutum mai suna Adamu Fasaha.

Source: Facebook
A cikin takardar ƙarar mai lamba K/M-1974/2026, wadda aka shigar a ranar 3 ga Agusta, 2026, mai ƙarar ya wallafa a Facebook cewa ya shigar da ƙarar ne domin kare haƙƙin Pantami.
Zargin da aka yi wa Rarara
A cewar takardar ƙarar, Sirajo Abubakar ya zargi waɗanda ake ƙarar da tsara, wallafa da yaɗa wasu waƙoƙi da bidiyoyi da yake cewa suna nuna Pantami a matsayin mai amfani da miyagun ƙwayoyi, mashayi, ɓarawo da kuma wanda ya mallaki kadarori ta hanyar kuɗin cin hanci.
Takardar ta kuma ce ana yawan kiran Pantami da kalmar "Pantsami", wadda mai ƙarar ya bayyana a matsayin wata kalma ta wulaƙanci da ake amfani da ita wajen tozarta shi.
Mai ƙarar ya ce irin waɗannan kalamai da hotuna da waƙoƙi sun jefa Pantami cikin zargi, wulaƙanci da tozarci a gaban jama'a, tare da rage darajarsa da mutuncinsa.
Abin da mai ƙarar ke nema
Daga cikin abubuwan da Sirajo Abubakar ya roƙi kotun ta yi akwai bayyana cewa Pantami yana da cikakken haƙƙin samun kariya daga duk wani abu da zai tauye masa mutuncin ɗan Adam, kamar yadda Sashe na 34 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada.

Source: Facebook
Ya kuma nemi kotu ta bayar da umarnin da zai hana Rarara da Adamu Fasaha, da duk wani mai aiki a ƙarƙashinsu, ci gaba da samarwa, yaɗawa ko watsa duk wani waƙa, bidiyo, sauti ko wani abu da ke danganta Pantami.
An so Rarara ya ba da N100bn
Mafi girman buƙatar da aka gabatar a ƙarar ita ce neman a umarci waɗanda ake ƙarar da su biya Pantami jimillar N100 biliyan.
A takardar, an bayyana kuɗin a matsayin diyya ta gama-gari, mai tsanani da kuma ta musamman saboda abin da mai ƙarar ya bayyana a matsayin take haƙƙin Pantami na mutuncin ɗan Adam.
Ana kuma neman a tilasta wa waɗanda ake ƙarar su janye kalaman da aka wallafa tare da neman afuwar Pantami a bainar jama'a.
A cewar ƙarar, ya kamata a wallafa wannan uzuri aƙalla a jaridu guda biyar, da kuma shafukan sada zumunta na waɗanda ake ƙarar, ciki har da Facebook, TikTok, YouTube, Instagram da X.
PDP ta soki kalaman Rarara
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP a Jihar Gombe ta yi Allah-wadai da kalaman da ta bayyana a matsayin na cin mutunci da Dauda Kahutu Rarara ya yi kan ɗan takararta na gwamnan jihar, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami.
Sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar a jihar, Abdulkadir Ahmad Dukku, ya ce kalaman da ke cikin wata waƙar da mawaƙin ya fitar sun ci mutuncin Pantami kuma suna da nufin ɓata masa suna.
Jam'iyyar ta ce bambancin ra'ayin siyasa bai kamata ya zama dalilin kai hari ga mutunci ko martabar wani ɗan siyasa ba, tana mai jaddada cewa ya kamata a gudanar da siyasa cikin mutunci da girmama juna.
Asali: Legit.ng


