Yan Sandan Jihohi: Barau Jibrin Ya Fadi Amfanin Shirin ga Arewacin Najeriya

Yan Sandan Jihohi: Barau Jibrin Ya Fadi Amfanin Shirin ga Arewacin Najeriya

  • Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya yi magana kan rundunar 'yan sandan jihohi a Najeriya
  • Barau ya ce hakan zai ƙarfafa tsaro tare da kawo zaman lafiya mai ɗorewa musamman a Arewacin Najeriya
  • Sanatan ya bayyana cewa kudirin ya samu shawarwari daga bangarori daban-daban, tare da sanya matakan kariya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu na kafa rundunar 'yan sandan jihohi.

Barau Jibrin ya ce hakan wata muhimmiyar dabara ce na ƙarfafa tsarin tsaro tare da taimakawa wajen magance matsalar rashin tsaro, musamman a Arewacin Najeriya.

Barau Jibrin ya fadi amfanin yan sandan jihohi
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin. Hoto: Barau I Jibrin.
Source: Facebook

Barau ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook bayan hira da yan jarida Kaduna.

Kara karanta wannan

Tinubu/Shettima: Matsayar Kiristocin Arewa kan sake daukar Kashim a mataimaki

Musabbabin kafa yan sandan jihohi

Ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu ce ta gabatar da kudirin bayan doguwar tattaunawa da Fadar Shugaban Ƙasa, Majalisar Tarayya, Sufeto Janar na 'Yan Sanda, tsofaffin jami'ai, masana harkokin tsaro, gwamnoni, ƙungiyoyin farar hula da sauran jama'a.

Barau, wanda kuma ke jagorantar Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki na Majalisar Dattawa, ya ce an gudanar da sauraron ra'ayoyin jama'a a dukkan shiyyoyin siyasar Najeriya da Babban Birnin Tarayya kafin a tsara kudirin.

Ya ce Shugaba Tinubu ya fahimci cewa mutane da dama suna goyon bayan rundunar 'yan sandan jihohi, amma suna tsoron kada gwamnoni su yi amfani da ita wajen siyasa ko nuna wariya. Saboda haka, an tanadi matakan kariya domin hana duk wani cin zarafi.

Barau ya ce rundunar 'yan sandan jihohi ba za ta maye gurbin rundunar 'yan sandan tarayya ba.

Ya bayyana cewa jami'an jihohi za su fito ne daga al'ummomin da za su yi aiki a cikinsu, lamarin da zai taimaka wajen yaƙi da 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu laifi.

Kara karanta wannan

'Kar mu ji, kar mu gani': Atiku ya gargadi gwamnati game da Obi, El Rufa'i

Amfanin yan sandan jihohi ga Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: UGC

Abin da zai jawo kwace iko daga gwamnoni

Ya ƙara da cewa idan aka yi ƙoƙarin amfani da rundunar jiha wajen zalunci ko barazana ga rayuka da dukiyoyi, kundin tsarin mulki zai ba Shugaban Ƙasa damar umartar rundunar tarayya ta karɓi iko.

Haka kuma, ya ce rundunar tarayya za ta ci gaba da kula da laifukan ta'addanci da na yanar gizo, yayin da rundunar jiha za ta mai da hankali kan tsaron cikin gida da tabbatar da zaman lafiya.

Barau ya kuma ce za a tsara yadda za a naɗa kwamandojin rundunar jihohi cikin gaskiya tare da kare su daga tsoma bakin siyasa.

Ya amince akwai ƙalubalen kuɗi da gudanarwa, amma ya ce za a samar da tsarin da ya dace yayin ci gaba da gyaran kundin tsarin mulki da sauran dokokin da suka shafi kudirin.

A ƙarshe, ya bukaci 'yan Najeriya da su mara wa wannan gyara baya, yana mai cewa lokaci ya yi da za a sake fasalin tsarin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi tare da tabbatar da cewa an hana duk wani amfani da rundunar ba bisa ƙa'ida ba.

Kara karanta wannan

Majalisa na neman taka wa Tinubu birki kan tubabbun yan ta'adda a Najeriya

Gwamnati ta magantu kan yan sandan jihohi

An ji cewa fadar Shugaban Kasa a Najeriya ta yi karin haske game da shirin kafa ƴan sanda a fadin jihohin kasar.

Gwamnatin ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba wajen kafa ‘yan sandan domin inganta tsaro a kasar.

An ce tattaunawar kafa ‘yan sandan ta fara watanni da suka gabata bisa umarnin Bola Tinubu, yanzu ya kai matakin gyaran doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com