Dalilin Najeriya na Bude 'Kofar Tuba ga 'Yan Bindiga a Najeriya
- Rundunar sojin Najeriya ta ce duk wata ƙungiya mai ɗauke da makamai za ta iya miƙa wuya a ko'ina cikin ƙasar, lamarin da ya ke sosa ran wasu yan kasar nan
- Hedikwatar Tsaro ta ce sabon tsarin ya shafi yankunan Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma domin a rage matsalar tsaro
- Sojoji sun ce za a bi dokokin ƙasa da ƙasa kafin a miƙa masu miƙa wuya ga hukumomin da suka dace domin a dauki matakan da suka dace a gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Rundunar sojin Najeriya ta sanar da faɗaɗa tsarin karɓar masu miƙa wuya daga cikin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai zuwa dukkan sassan ƙasar.
A cikin ƴan shekarun nan, yankin Kudu maso Gabas ya kasance cikin yankunan da suka fi fuskantar hare-hare kan jami'an tsaro, cibiyoyin gwamnati da kuma fararen hula.

Source: Facebook
BBC Hausa ta kawo labarin cewa domin dakile wannan matsala, rundunar ta ƙaddamar da Operation UDO KA, wadda aka kafa domin tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifuka da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.
Najeriya na kokari kan yan bindiga
Sai dai yanzu rundunar ta bayyana cewa tsarin karɓar masu miƙa wuya ba ya taƙaita ga yankin Kudu maso Gabas kaɗai, domin an faɗaɗa shi zuwa dukkan wuraren da sojoji ke gudanar da ayyuka a Najeriya.
Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya ce duk wata ƙungiya mai ɗauke da makamai a Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma na da damar miƙa wuya

Source: Facebook
Da aka tambaye shi ko an faɗaɗa tsarin zuwa sauran yankunan ƙasar, ya amsa da cewa:
"Eh. Muna maraba da duk wanda ya miƙa wuya."
Janar Onoja ya bayyana cewa rundunar za ta karɓi duk wanda ya miƙa wuya bisa tanadin dokokin ƙasa da ƙasa da kuma Yarjejeniyoyin Geneva, kafin daga bisani a miƙa shi ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar matakin doka.
Ya ƙara da cewa rundunar sojin Najeriya na gudanar da ayyukanta ne bisa ƙa'idojin aikin soja, dokokin jin ƙai na ƙasa da ƙasa da kuma Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
Sojoji sun samu nasarori
Rundunar ta ce wannan mataki ya biyo bayan nasarorin da aka samu a ƙarƙashin Operation UDO KA, inda hare-haren da sojoji suka kai suka tilasta wa wasu mayaƙa a yankin Kudu maso Gabas miƙa wuya.
Ta kuma bayyana cewa bayan miƙa wuya, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi ya jagoranci dakarun soji zuwa ma'ajiyar makaman ƙungiyar.
Masana harkokin tsaro sun ce dokokin yaƙi na ƙasa da ƙasa, musamman Yarjejeniyoyin Geneva, sun tanadi cewa duk mayaƙin da ya miƙa wuya ko aka kama shi bayan ya daina faɗa dole ne a kare rayuwarsa tare da yi masa mu'amala cikin mutunci.
Sai dai sun jaddada cewa miƙa wuya ba ya nufin za a yafe wa mutum duk wani laifi da ake zarginsa da aikatawa, domin hukuncin hakan ya dogara ne da dokokin ƙasa da kuma irin laifukan da ake zargin ya aikata.
Sojoji sun yi arangama da yan bindiga

Kara karanta wannan
2027: Yadda Tinubu, Atiku da sauran ƴan takara ke shirin amfani da tsofaffin gwamnoni
A baya, mun kawo labarin cewa dakarun rundunar sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 14 da aka yi garkuwa da su bayan sun fafata da ƴan bindiga a wata ƙaramar hukuma a Sakkwato.
Sojojin sun kuma ƙwato shanu 195, tumaki 84, raƙuma biyu da babura biyu bayan maharan sun tsere sakamakon luguden wutar da aka yi musu wanda ya gigita jamaa da hana su sukuni.
Jami'an tsaro sun ce haɗin gwiwar al'umma da bayanan sirri ne suka taimaka wajen samun nasarar wannan samame a yankin, tare da bukatar jama'a da su ci da bayar da hadin kai da bayanan sirri.
Asali: Legit.ng

