Gwamnatin Tinubu Ta Yi Korafi kan NBAIS da Sardauna Ya Kafawa Musulmi a 1960

Gwamnatin Tinubu Ta Yi Korafi kan NBAIS da Sardauna Ya Kafawa Musulmi a 1960

  • Sanata Kawu Sumaila ya nuna adawa da korafin Ministan shari'a kan hukumar NBAIS da da ke lura da karatu da jarrabawar dalibai Musulmi a Najeriya
  • Da ya ke magana a zauren majalisa, Kawu Sumaila ya bayyana cewa bai kamata anuna adawa da hukumar da ta shafe shekara da shekaru tana aiki ba
  • Bincike ya nuna cewa Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello ne ya kafa hukumar a shekarar 1960 domin kawo cigaba a harkokin ilimi a Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sanata Kawu Sumaila ya yi korafi kan bukatar ministan shari’a, Lateef Fagbemi dangane da hukumar kula da nazarin Larabci da addinin Musulunci ta kasa (NBAIS).

Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila, OFR, ya jawo hankalin ministan shari’a kan muhimman ƙa’idoji da dokokin da suka shafi NBAIS.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Peter Obi ya bayyana abin da zai fara yi game da Nnamdi Kanu

Ofishin NBAIS a jihar Kano
Ofishin hukumar NBAIS da aka sabunta a jihar Kano. Hoto: National Board for Arabic and Islamic studies - NBAIS
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da sanatan ya yi a majalisa ne a wani sako da shafin Kawu Sumaila Repoters ya wallafa a Facebook.

NBAIS: Korafin Sanata Kawu Sumaila

Yayin da yake korafi game da bukatar gwamnatin Najeriya, Sanata Kawu Sumaila ya bayyana cewa ofishin shugaban ma'aikata na Najeriya ma yana sane da zaman hukumar.

Ya ce hukumar tana da hedkwata a Kaduna da kuma ofisoshi a dukkan sassan Najeriya kuma ta kasance tana aiki a kasar nan sama da shekara 60 da suka wuce.

Sanata Sumaila ya bayyana cewa a yanzu haka hukumar ta gudanar da jarrabawa dimbin dalibai a makarantu sama da 1,000 a jihohi 30 a Najeriya.

A kan haka sanatan ya ce ayyukan hukumar sun dace da manufar gwamnatin Bola Tinubu ta habaka ilimi da yaki da jahilci a Najeriya.

Bayani game da hukumar NBAIS

Hukumar kula da nazarin Larabci da addinin Musulunci ta kasa (NBAIS) hukuma ce ta Gwamnatin tarayya mai gudanar da jarrabawa.

Kara karanta wannan

June 12: Tinubu ya ce a caccake shi, amma ya fadi abin da ba ya so a yi

NBAIS na da alhakin daidaita tsarin karatu da bayar da takardun shaidar karatun Larabci da na addinin Musulunci a faɗin Najeriya.

Marigayi Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello ne ya kafa ta a shekarar 1960, sannan aka mayar da ita ƙarƙashin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1969.

A wani sakon da ta wallafa a shafinta, hukumar ta ce tun daga lokacin, hukumar ta samu sauye-sauye masu amfani da ci gaba.

Sanata Kawu Sumaila
Sanata Kawu Sumaila yana amsa waya. Hoto: Kawu Sumaila Reporters
Source: Twitter

Da farko, hukumar ta kasance mai kula da Arewacin Najeriya ne kawai, tare da 'yan makarantu da kwalejoji kaɗan a ƙarƙashinta.

Amma a yau, bayan amincewa da ita da majalisar ilimi ta kasa (NCE) ta yi a taronta na 57 da aka gudanar a Sokoto a watan Fabrairu na shekarar 2011, hukumar tana aiki a matsayin hukumar jarrabawa ta kasa.

Rahotanni sun nuna cewa a yanzu haka, NBAIS na kula da dubban makarantu da kwalejoji da aka amince da su a faɗin ƙasar.

Ana son hana shigo da tufafi

A wani labarin, mun kawo muku cewa Majalisar dattawa ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya hana shigo da yadi daga ketare.

Kara karanta wannan

"Talauci da jahilci sun yi kamari a Arewa": Sarki Sanusi II ya ba da mafita

Ta bayyana cewa daukar matakin zai taimaka wajen farfado da masana'atun Najeriya wanda hakan zai kai ga habaka tattalin kasar.

A bangare guda kuma, majalisar ta sanar da cewa hana shigo da yadi daga kasashen waje zai taimaka wajen bunkasa noman auduga a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng