Sarkin Musulmi Ya Kausasa Kurya kan 'Yan Bindiga, Ya Ce a Hada Kai a Yake Su

Sarkin Musulmi Ya Kausasa Kurya kan 'Yan Bindiga, Ya Ce a Hada Kai a Yake Su

  • Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar III ya yi kira ga dukkan 'yan Arewa da su hada kai wajen yakar 'yan bindiga
  • Sultan ya yi wannan kira ga jama'ar Arewa ne a taron hadin gwiwa na sarakunan Arewa da gwamnoni da aka yi a Kaduna
  • Ya kuma nemi gwamnonin Arewa su ba da kudi mai yawa domin tabbatar da nasarar sabon kwamitin tsaro na yankin da aka kafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III, ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a yankin Arewa da su hada kai wajen adawa da matsalar 'yan bindiga, ta'addanci da satar mutane.

Sultan ya bayar da wannan jawabi ne a ranar Laraba a taron hadin gwiwa da aka gudanar a birnin Kaduna, inda sarakunan gargajiya da gwamnonin yankin Arewa suka hadu.

Kara karanta wannan

Da gaske alkalin da ya ba Tinubu nasara a kotu a zaben 2023 ya makance?

Mai alfarma Sarkin Musulmi a wajen taro
Lokacin da Sultan ke jawabi. Hoto: Jama'atu Nasril Islam
Source: Facebook

A sakon da JNI ta wallafa a Facebook, Sultan ya bayyana cewa tsaro ya zama aikin dukan al'umma, ba na hukumomi ko gwamnoni ko sarakuna kadai ba.

Ya kuma lissafa cewa babbar hanyar da za a bi wajen magance matsalar tsaro ita ce ta hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci, rundunonin tsaro, cibiyoyin gargajiya da kuma sauran jama'a.

Sabon kwamitin tsaron Arewa

Babban abin da ya janyo hankalin taron shi ne kaddamar da wata kwamitin amintattu, wanda za ta jagoranci ayyukan da suka shafi tsaro a yankin.

Daily Truts ta rahoto cewa Sarkin Musulmi ya yi murna da wannan matakin, yana mai cewa yana nuna sahihiyar niyya ta fara aiki kan wannan babban kalubale.

Kwamitin da aka kaddamar ta kunshi fitattun mutane daga jihohin Arewa guda 19 baki daya. Sultan ya tabbatar wa membobinta cewa za su samu hadin kai daga wajen sarakunan gargajiya a duk lokacin da suka bukata.

Kara karanta wannan

An bankado wurare masu hadari a Abuja, an kama mutum 560 da bindigogi

Ya kara da cewa sarakunan gargajiya sun dade suna gargadi game da hadarin tsattsauran ra'ayi, har ma a shekarar 2014 suka miqa takardar shawarwari game da matsalar tsaro zuwa ga majalisar gwamnonin Arewa.

Batun hada kai a Arewa

Sultan ya jaddada cewa gwagwarmayar yaki da rashin tsaro ba za ta yiwu ta tsaya kan bambancin addini ko kabilanci ba. Ya nuna cewa hadin kan jihohin Arewa guda 19 a kwamitin shi ne ginshikin da za a gina nasara a kansa.

Ya yi kira da musamman ga gwamnonin Arewa da su bayar da kudi domin tabbatar da nasarar wannan sabon shiri na tsaro, yana mai cewa idan ba kudi, babu abin da za a cimma.

Malaman da Sarkin Musulmi ya tara a Kaduna
Lokacin da Sarkin Musulmi ya tara malamai don tattauna matsalolin Arewa a Kaduna. Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Facebook

An kafa asusun tsaro a 2025

A baya, a watan Disamban 2025, mun kawo muku cewa gwamnonin jihohin Arewa sun amince da kafa asusun tsaro domin samar da kuɗin gudanar da ayyukan tsaro na haɗin gwiwa.

A ƙarƙashin tsarin, ana sa ran kowace jiha tare da ƙananan hukumominta za su riƙa ba da gudummawar Naira biliyan 1 a kowane wata, inda za a riƙa cire kuɗin kai tsaye bisa tsarin da aka amince da shi.

An cimma wannan matsaya ne a yayin wani taron haɗin gwiwa tsakanin gwamnonin jihohin Arewa da sarakunan gargajiya a Kaduna, inda shugabannin suka bayyana cewa asusun zai ƙarfafa haɗin kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng