'Yan Tijjaniyya daga Kasashen Duniya Sun Turo Sako Ga Tinubu kan Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

'Yan Tijjaniyya daga Kasashen Duniya Sun Turo Sako Ga Tinubu kan Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

  • Majalisar Koli ta Tijjaniyya ta duniya ta kai wa Shugaba Bola Tinubu ziyarar ta'aziyya kan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a Aso Rock
  • Tawagar daga Aljeriya, Najeriya da Senegal ta wakilci sama da mambobi miliyan 400 na darikar a duniya wajen mika sakon ta'aziyya ga Tinubu
  • Shugaban Najeriya, Bola Ajmed Tinubu ya yabawa ayyukan addinin Musulunci da darikar Tijjaniyya ke gudanarwa a Afirka da ma duniya baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Majalisar Koli ta Darikar Tijjaniyya ta duniya ta kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ziyara a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Shugabannin darikar Tijjaniyya na duniya sun mika sakon ta'aziyya kan rasuwar marigayi Sheikh Dahiru Bauchi, tsohon jagoran darikar Tijjaniyya a Najeriya ga Shugaba Tinubu.

Abuja.
Shugabannin Darikar Tijjaniyya tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja Hoto: @DOLusegun
Source: Twitter

Tawagar Tijjaniyya ta ziyarci Bola Tinubu

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi babban rashi, Dr. Adamu Mohammed Fika ya riga mu gidan gaskiya

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa na mussmman kan harkokin midiya da sadarwa, Sunday Dare ya wallafa a shafin X yau Juma'a, 7 ga watan Agusta, 2026.

Tawagar ta kunshi wakilai daga kasashe uku, Aljeriya, Najeriya da Senegal, tare da mambobin Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi karkashin jagorancin Khalifa Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

An bayyana cewa tawagar tana wakiltar sama da mambobi miliyan 400 na darikar a duniya.

Khalifan Tijjaniyya ya isar da sakon ta'aziyya

Khalifan Darikar Tijjaniyya daga Aljeriya, Sheikh Ali Bin Arabi, ne ya isar da sakon ta'aziyyar ga Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Sheikh Ali Bin Arabi ya bayyana irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin Najeriya da Aljeriya, yana mai cewa za su ci gaba da yin addu'ar dorewar alakar addini tsakanin kasashen biyu.

Ya kuma yi wa Shugaba Bola Tinubu addu'ar samun zaman lafiya, soyayya, lafiya ta jiki da ta ruhaniya.

Tinubu ya yabawa darikar Tijjaniyya

Da yake mayar da martani, Shugaba Tinubu ya gode wa tawagar bisa ziyarar ta'aziyyar.

Bola Tinubu ya ce:

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin marigayi Buhari ta kashe N1.16trn na tallafin man fetur

"Muna matukar kewar mahaifinmu, Sheikh Dahiru Bauchi. Ya kasance uba abin kauna kuma babban jagora."

Shugaban kasar ya kuma yabawa Darikar Tijjaniyya kan ayyukan da take yi wajen yada addinin Musulunci.

"Ina girmama ku saboda abin da kuke yi domin Musulunci a fadin Afirka da ma duniya baki daya. Allah Ya ci gaba da yi muku jagora," in ji shi.
Dahiru Bauchi.
Marigayi jagoran darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi Hoto: Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi
Source: Twitter

Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu a 2025

Bayanai sun nuna cewa cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu ne a ranar 26 ga Nuwamba, 2025, yana da shekaru 98 a duniya.

Rasuwar babban malamin ta jawo hankalin duniya, inda aka rika turo sakon ta'aziyya daga ciki da wajen Najeriya.

Abin iyalan Dahiru Bauchi suka fadawa Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa iyalan fitaccen malamin addinin Musulunci, marigayiSheikh Dahiru Usman Bauchi , sun bayyana mutanen da suka amfani da koyarwarsa.

Iyalan sun bayyana cewa mahaifinsu ya yi jagoranci tare da tarbiyya ga Musulmi sama da miliyan 63 a fadin Najeriya da wasu sassan duniya a tsawon rayuwarsa.

Sun bayyana hakan ne lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar ta’aziyya biyo bayan rasuwar babban malamin addinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262