Mai Dokar Barci: Kotu Ta Daure Babban Jami'in NSCDC
- Wata kotu da ke jihar Katsina ta samu mataimakin kwamandan hkumar tsaron fararen hula, NSCDC, Sani Lawal, da laifin damfara
- Kotun ta same shi da laifin damfara, inda ya karɓi N920,000 daga wasu matasa masu neman aikin yi da alƙawarin samar masu aiki a NSCDC
- Hukumar da ke yaki yi wa kasa ta'annati cewa hukumar ICPC ta gargaɗi 'yan Najeriya da su guji biyan kuɗi ga masu alƙawarin ba su aikin gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – Babbar Kotun Jihar Katsina ta yanke wa Mataimakin Kwamandan Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), Sani Lawal, hukunci bayan ta same shi da laifin damfarar neman aiki.
Mai shari'a A.A. Bawale ne ya yanke hukuncin bayan ya tabbatar da tuhume-tuhumen da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta shigar a kansa.

Kara karanta wannan
An yi walƙiya: ADC ta nemi Tinubu ya yi wa El Rufa'i yadda aka yi wa gwamnatin Osun

Source: Twitter
The Guardian ta wallafa cewa ICPC ta ce, laifukan sun saɓa wa Sashe na 25(1)(a) na Dokar Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka masu Alaƙa ta shekarar 2000, kuma ana hukunta su ƙarƙashin Sashe na 25(1)(b) na dokar.
An daure jami'in NSCDC
Jaridar The Nation ta kawo labarin cewa lauyan ICPC, Haruna Hedima, ya shaida wa kotu cewa wanda ake tuhuma ya karɓi kuɗi har N920,000 daga wasu mutane biyu a shekarar 2024.
Ya kara da cewa babban jami'in hukumar ya rika yi masu ƙarya cewa zai samar musu aiki a hukumar tsaron fararen hula ta kasa, NDCDC.
Ko da yake tun farko ICPC ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume takwas, hukuncin ya ta'allaka ne kan tuhume-tuhume biyu bayan ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar amsa laifi wadda kotu ta amince da ita.
A hukuncinsa, Mai shari'a Bawale ya same shi da laifin damfarar mutane da zummar sama masu aikin yi tare da yanke masa tarar N100,000.
Alƙalin ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan yarjejeniyar amsa laifi da masu gabatar da ƙara da lauyan wanda ake tuhuma suka cimma, wadda kotu ta amince da ita.
ICPC ta gargadi jama'a
A cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a na ICPC, J. Okor Odey, ya fitar, hukumar ta ce tsarin ɗaukar ma'aikatan gwamnati yana da ƙa'idoji da matakai da aka tanada, ba ta hanyar biyan kuɗi ba.

Source: Original
Ya ce:
"Hukumar ICPC na ci gaba da jajircewa wajen bincike da gurfanar da duk masu hannu a ayyukan cin hanci da rashawa, kuma muna ƙarfafa jama'a su riƙa kai rahoton irin waɗannan laifuka ta hanyoyin da muka tanada."
ICPC ta gargaɗi 'yan Najeriya da su yi taka-tsantsan da mutanen da ke karɓar kuɗi ko wata kyauta da sunan za su samar musu aiki a ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati.
Yadda alkali ya tsere a Katsina
A baya, mun kawo labarin cewa wani alƙalin kotun Shari'a a ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina ya tsallake rijiya da baya bayan 'yan bindiga sun kai hari kotun tare da gigita jama'a.
Alƙalin ya tsere ta taga kafin maharan su shiga kotun, inda suka riƙa harbe-harbe suna neman inda yake, lamarin ya sake ƙara fargaba a Katsina, shekaru biyar bayan da wasu 'yan bindiga suka sace wani alƙalin kotun Shari'a.
Wani shaidar gani da ido kuma ya ce maharan sun fusata bayan sun gano cewa alƙalin ya tsere. A cewarsa, sun yi barazanar kashe alƙalin idan ya sake dawowa domin ci gaba da zaman kotu a ƙauyen.
Asali: Legit.ng

