Manyan Labarai A Yau
A yan makonnin nan ne kungiyar ciniki ta duniya watau WTO ta sake naɗa Dr. Ngozi a karo na biyu, mun tattaro maku ƴan Najeriya da ke riƙe da muƙamai a duniya.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fito ta musanta rahotannin da aka yada kan cewa shugabanta, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi bankwana da duniya.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi rabon mukami a gwamnatinsa. Gwamna ya nada mai ba shi shawara na musamman kan harkokin kananan hukumomi.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya umarci a biya ma'aikatan jihar albashin watan Disamban 2024 da wuri domin bukukuwan da kw tafe.
Naira tiriliyan 3 ya shigo cikin asusun gwamnatin tarayya kuma an raba Naira tiriliyan 1.7 a FAAC. Gwamnatin tarayya ta samu N580bn, an raba N549bn a jihohi.
Gwamnatin tarayya ta zargi Facebook da sabawa ka'idoji don haka aka ci ta tara. A yanzu alkali ya bukaci hukumar ARCON ta bar magaar wannan haraji na N60bn.
Miinistan shari'a, Lateef Fagbemi, ya ja kunnen shugabannin kananann hukumomi kan yin almundahana da kudaden jama'a. Ya ce za a tura su gidan yari.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya fadi dalilin da ya sanya Shugaba Bola Tinubu ya ba Nyesom Wike minista a gwamnatinsa.
Dakarun sojojin Najeriya sun ci gaba da bude wuta kan 'yan ta'addan Lakurawa. Sojojin sun lalata sansanonin 'yan ta'addan da ke a jihohin Kebbi da Sokoto.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari