Gwamna Dauda Lawal Ya Tirje, Ya Yi Magana kan Sulhu da ƴan Bindiga a Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Tirje, Ya Yi Magana kan Sulhu da ƴan Bindiga a Zamfara

  • Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi magana kan yin sulhu da ƴan bindiga ba, sai dai su miƙa wuya ko su fuskanci hukunci
  • Babban Sakataren Gwamnan, Mukhtar Musa, ya ce gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa jami'an tsaro da kayan aiki, alburusai da sauran buƙatun yaƙi
  • Gwamnatin Zamfara ta ba ƙungiyar 'yan asalin jihar da ke Kaduna gudummawar Naira miliyan biyar, yayin da aka raba kayan abinci ga marasa galihu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Gusau, Zamfara - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi martani game da yin sulhu da ƴan bindiga a jiharsa.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa yin sulhu da ƴan bindiga ba.

Gwamna Dauda ya magantu kan sulhu da ƴan bindiga
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara. Hoto: Dauda Lawal.
Source: Facebook

Babban Sakataren Gwamnan, Mukhtar Musa, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da sakatariyar ƙungiyar ƴan asalin Zamfara mazauna Kaduna, cewar Punch.

Kara karanta wannan

"Babu sulhu": Gwamna Dauda ya fadi shirinsa kan kawo karshen 'yan bindiga

Ƴan bindiga sun banu a jihar Zamfara

Ya ce za a ci gaba da kai musu hare-haren soji har sai sun miƙa wuya ko kuma sun fuskanci cikakken hukuncin doka.

Taron ya kuma haɗa da rabon kayan abinci ga marasa galihu daga cikin mambobin ƙungiyar.

Mukhtar Musa ya ce gwamnatin Dauda Lawal na ci gaba da jajircewa wajen kawo ƙarshen rashin tsaro ta hanyar haɗin gwiwa da hukumomin tsaro a faɗin Zamfara.

Ya bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da samar wa jami'an tsaro kayan aiki, alburusai, kayan sufuri da sauran tallafin da suke buƙata domin yaƙi da masu aikata laifuka.

Ya ce:

"Gwamnan ba zai taɓa yin sulhu da ƴan bindiga ba, duk wanda yake son miƙa wuya ya yi hakan, in ba haka ba ya fuskanci hukuncin doka."
Zamfara ta yi magana kan sulhu da ƴan bindiga
Taswirar jihar Zamfara da ke fama da matsalar tsaro. Hoto: Legit.
Source: Original

Alwashin da gwamnatin Zamfara ta sha

Mukhtar Musa ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da kai farmaki kan ƴan bindiga har sai an tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a dukkan sassan Zamfara.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka barna a Sokoto, sun kashe basarake, ɗansa da wasu mutane

Ya ce bayanan sirri daga mazauna yankuna na da matuƙar muhimmanci wajen samun nasara a yaƙi da rashin tsaro.

Saboda haka ya buƙaci al'umma su riƙa gaggauta sanar da jami'an tsaro duk wani motsi ko aiki da suke zargi domin ɗaukar matakin gaggawa.

Ya tabbatar wa mambobin ƙungiyar cewa gwamna na ci gaba da ƙoƙarin samar da ci gaba mai ma'ana tare da dawo da zaman lafiya a Zamfara.

Mukhtar Musa ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki da ke nuna haɗin kai tsakanin ƴan asalin Zamfara da ke zaune a wajen jiharsu.

Ya yaba wa waɗanda suka shirya taron bisa nasarar kafa sakatariyar ƙungiyar a Kaduna.

Ya kuma tabbatar da cewa Gwamna Dauda Lawal zai kai wa ƙungiyar ziyara nan gaba domin ƙarfafa dangantaka da haɗin kai.

Gwamna Radda zai yi sulhu da yan bindiga

An ji cewa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya aika sako ga 'yan bindigan da ke kai hare-hare kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Kara karanta wannan

Dan a mutun Tinubu ya kare Oluremi, ya ba da labarin attajira mai sayar da ƙosai a Abuja

Dikko Radda ya bukaci 'yan bindigan da su ajiye makamansu domin rungumar zaman lafiya da daina aikata barna.

Gwamnan ya nuna cewa kofa a bude take ga duk wadanda suka rungumi zaman lafiya domin samun hanyar shiga cikin al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com