Bauchi: Bala Mohammed Ya Yi Garambawul a Majalisar Zartarwa, Ya Sauke Kwamishinoni 2

Bauchi: Bala Mohammed Ya Yi Garambawul a Majalisar Zartarwa, Ya Sauke Kwamishinoni 2

  • Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya yi ƙaramin garambawul a majalisar zartarwar jihar inda ya raba wasu daga cikin kwamishinoninsa da kujerunsu
  • Haka kuma an samu 'daya daga cikin kwamishinoninsa ya yi murabus, kuma gwamnan ya amince da ajiye mukaminsa da ya yi nan take
  • A yanzu haka, an tura sunayen sababbin waɗanda aka zaɓa zuwa Majalisar Dokokin Bauchi domin tantancewa da amincewa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya amince da yin ƙaramin garambawul a majalisar zartarwar jihar, inda kwamishinoni biyu suka bar mukamansu, sannan ya amince da murabus na wani kwamishina.

Mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Mukhtar Gidado, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a 17 ga watan Yuli, 2026.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: "Akwai kalubale kan tikitin Obi da Kwankwaso"

Gwamna Bala Mohammed ya yi garambawul a gwamnatinsa
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Hoto: Senator Bala AbdulKadir Muhammad
Source: Twitter

Nigerian Tribune ta wallafa cewa ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na ƙara inganta shugabanci da kuma samar da ingantaccen aiki ga al'ummar Bauchi.

Dalilin Gwamnatin Bauchi na garanbawul

A cewar sanarwar, an dakatar da Kwamishinan Kasuwanci, Masana'antu da Zuba Jari, Mohammed Salis Gamawa, da tsohon Kwamishinan Ilimi, Dakta Lawal Rimin Zayam, wanda daga baya aka mayar da shi Ma'aikatar Wutar Lantarki, Kimiyya da Fasaha.

A cewar sanarwar, gwamnan ya amince da murabus ɗin tsohon Kwamishinan Raya Karkara da Ayyuka na Musamman, Faruk Mustapha.

Sanarwar ta bayyana cewa Gwamna Bala Mohammed ya aika da sunayen waɗanda aka zaɓa domin maye gurbin waɗanda aka sallama ga majalisa.

An tura sunayen yan majalisa Bauchi

Sanarwar ta kuma ce an aika sunayen waɗanda za su cike guraben da aka samu a majalisar zartarwar jihar, zuwa Majalisar Dokokin Jihar Bauchi.

Gwamna Bala Mohammed ya ce an yi garambawul don ci gaban gwamnati
Gwamna Bala Mohammed ya na jawabi a gidan gwamnatin Bauchi Hoto: Senator Bala AbdulKadir Mohammed
Source: Facebook

Ana sa ran majalisar za ta tantance su tare da ba su amincewar da doka ta tanada kafin su fara aiki yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

An yi kicibis, sojoji sun yi ram da 'dan bindiga a hanyar sintiri

Gidado ya ce matakin ya dace da manufar gwamnatin jihar ta tabbatar da ci gaba da gudanar da mulki cikin inganci da kuma ba tare da tangarda ba.

Gwamna Bala Mohammed ya gode wa kwamishinonin da suka bar mukamansu bisa gudummawar da suka bayar wajen ci gaban jihar Bauchi.

An rubuta wa Gwamnan Bauchi wasika

A baya, mun kawo labarin cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya samu budaddiyar wasika daga wajen dansa, Shamsudeen Bala Mohammed inda ya ja hankalinsa game da ci gaban al'umma.

Yaron gwamnan ya yaba kan irin ayyukan raya kasa da nasararin da Gwamnan jihar Bauchi ya samu cikin shekaru bakwai a kan mulki sai dai, Shamsudeen ya kuma jawo hankalin Bala Mohammed kan wasu abubuwa.

Shamsudeen ya bayyana cewa ya rubuta wasikar ne domin bayyana ra'ayinsa cikin girmamawa, tare da nuna damuwa kan halin da ake ciki a Bauchi domin a kara samun ci gaban al'ummar jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng