Gwamnan Gombe Ya Bayyana Babban Abin da ke Hana Arewa Ci Gaba
- Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya bayyana yadda rashin tsaro ya zama babbar barazana da ke hana Arewacin Najeriya samun ci gaba
- Ya kara da cewa wannan babban al'amari, ganin yadda rashin tsaro ke tsayar da al'amura da kwanciyar hankali a tsakanin mazauna shiyyar
- Gwamna Inuwa Yahaya ya sanar da jama'a hanyar da za su bi wajen taimakon gwamnati da jami'an tsaro domin a gudu tare da tsira tare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa rashin tsaro ne ke zama babbar barazana ga zaman lafiya da ci gaban Arewacin Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wa al'ummar jihar domin ƙaddamar da kamfen ɗin "Unite Against Terror" da ke da nufin haɗa kan jama'a wajen yaƙi da ta'addanci da sauran manyan laifuka.

Kara karanta wannan
El Rufa'i: Dalilin kotu na ci gaba da fatali da bukatar belin tsohon gwamnan Kaduna

Source: Facebook
Rahoton da jaridar Punch ta wallafa ya bayyana cewa Gwamnan ya jaddada cewa samar da tsaro ba aikin gwamnati da jami'an tsaro kaɗai ba ne, illa alhakin kowa da kowa.
Yadda za a taimaki Arewa kan rashin tsaro
A ruwayar jaridar The Sun Nigeria Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana yadda jama'a za su hada hannu da gwamnati domin kawo karshen matsalar da ake fama da ita.
Ya ce:
"Tsaro alhakin kowa ne. Gwamnati da jami'an tsaro ba za su iya yin komai su kaɗai ba. Idan ka ga wani abu da ba ka yarda da shi ba, ka kai rahoto."
Gwamna Inuwa Yahaya ya ƙara da cewa duk wanda ya lura da wani motsi, taro ko wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiyar al'umma, ya kamata ya sanar da hukumomin tsaro cikin gaggawa.
Gwamna ya yabi dakaru kan tsaro
Gwamnan ya yabawa dakarun soji da sauran jami'an tsaro kan irin sadaukarwar da suke yi, tare da karrama waɗanda suka rasa rayukansu yayin gudanar da aikinsu.
A cewarsa:
"Rashin tsaro shi ne babbar barazana ga zaman lafiya da ci gaban Arewacin Najeriya. Idan babu tsaro, babu ci gaba, kuma idan babu ci gaba, ba za a samu zaman lafiya mai ɗorewa ba."
Ya buƙaci jami'an tsaro su ci gaba da amfani da fasahar zamani tare da bayanan sirri daga al'umma, amma cikin mutunta haƙƙin ɗan Adam.ss

Source: Original
Gwamnan ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya, malamai, matasa, ƙungiyoyin mata da ƙungiyoyin fararen hula su haɗa kai wajen inganta zaman lafiya.
A cewarsa:
"Masu aikata laifffuuka da 'yan ta'adda suna samun ƙarfi ne idan al'umma ta rabu. Amma suna kasa cimma burinsu idan jama'a sun haɗa kai kuma suna sanya ido."
Gwamna inuwa Yahaya ya magantu kan APC
A baya, mun kawo labarin cewa Shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe ya jaddada kira a zabi Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC a babban zaben 2027 mai zuwa a cikin 'yan watanni.
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana haka ne yayin taro da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC daga karamar hukumar Akko a jihar Gombe, inda ya yaba wa mutanen yankin kan yadda suke ba shi hadin kai wajen tafiyar da gwamnati.
Tawagar da ta halarci taron ta kunshi ‘yan majalisun tarayya da na jiha, manyan jiga-jigan jam’iyya, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da dimbin magoya bayan jam’iyya mai mulkin Najeriya ta APCS.
Asali: Legit.ng

