Abubawa 6 da Suka Jawo Cece Kuce kan Gwamnatin Najeriya a Makon nan

Abubawa 6 da Suka Jawo Cece Kuce kan Gwamnatin Najeriya a Makon nan

Abubuwa da dama sun dauki hankali a Najeriya, musamman a wannan mako da ake bankwana da ita wanda ya jawo cece-kuce a kan gwamnatin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Nigeria – Wasu daga cikin batutuwan sun fito ne daga Fadar Shugaban Kasa, inda zarge-zarge kan kafa wata ma'aikata ta bogi ya haddasa ce-ce-ku-ce a fadin kasar.

Manyan abubuwa shida sun jawo maganganu a Najeriya a makon da ya gabata
Shugaban Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Tinubu/ADC/Getty
Source: UGC

Haka kuma, kalaman Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Remi Tinubu, kan kananan sana'o'i sun jawo muhawara, yayin da aka samu sababbin bayanai kan sauya kayan aikin masu yi wa kasa hidima da sauransu.

Legit ta tattaro manyan batutuwan da suka fi daukar hankalin jama'a a cikin gida da wajen Najeriya a makon da ya gabata.

Batutuwan da suka jawo cece-kuce a Najeriya

Kara karanta wannan

An rike dan ta'adda da ya nufi fadar sarki da bindiga zai kai hari

1. Kalaman Remi Tinubu

A farkon makon da ya gabata ne Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Remi Tinubu, ta sake nanata magana bayan suka da ta fuskanta kan shawarar da ta ba mata marasa aikin yi.

A ruwayar Vanguard, Remi Tinubu bukaci mata su rungumi kananan sana'o'i kamar su soya kosai da gasa masara domin samun abin dogaro da kai, maimakon ci gaba da korafin rashin aikin yi.

Kalaman Uwargidan shugaban kasa sun yamutsa hazo a Najeriya
Matar Shugaban kasa, Oluremi Tinubu Hoto: Senator Oluraemi Tinubu
Source: Twitter

Sai dai kalaman nata sun jawo suka daga matasa da dama, wadanda suka zarge ta da rashin fahimtar irin mawuyacin halin tattalin arzikin da 'yan Najeriya ke ciki.

Da take magana a jihar Jigawa ranar Litinin 29 ga watan Yuni, 2026, Remi Tinubu ta ce ba su damu da sukar da ake yi mata ba, tana mai jaddada cewa gwamnati na ci gaba da kokarin inganta rayuwar al'umma.

2. Zargin kafa ma'aikatar bogi

An yamutsa hazo sosai a makon nan bayan Fadar Shugaban Kasa ta sanar cewa Adeniyi Adeyemi, ya assasa tare da nada kansa a matsayin Darakta Janar na wata hukuma PFIPC da kuma PEAC, duka kuma na bogi.

Kara karanta wannan

"Ni ba ungulu ba ne:" Ganduje ya yi martani ga zargin zai hade da Kwankwaso

Batun bude ma'aikata a Najeriya ya bayar da mamaki
Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da bude ma'aikata a Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar, gwamnatin tarayya ta ce 'yan sanda sun gurfanar da Adeyemi tare da wasu mutum biyu bisa tuhume-tuhume takwas.

Jaridar Leadership ta kawo labarin cewa sai dai Adeyemi ya musanta dukkannim zarge-zargen, yana mai cewa ya na da yakinin kotu za ta wanke shi daga abin da ake tuhumarsa da shi.

3. Zargin badakalar Gbajabiamila

Har ila yau, an yi ta ce-ce-ku-ce kan Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila inda jam'iyyun adawa suka neman a yi bincike a kansa.

Ana zargin Gbajabiamila da hannu a kafa PFIPC
Shugaban ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila Hoto: Femi Gbajabiamila
Source: Facebook

Abin da ya jawo wannan shi ne alakanta shi da badakalar da ta shafi hukumar PFIPC, tare da zargin cewa an samu almundahana da ta kai kusan Naira miliyan 400 da kuma daukar ma'aikata ba bisa ka'ida ba.

Jam'iyyar ta ce idan har zarge-zargen suka tabbata, za su haifar da tambayoyi masu yawa kan gaskiya, rikon amana da kuma tsarin gudanar da mulki na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Sheikh Mansur Sokoto: Ma'anar batanci ga Annabi Muhammad SAW da hukuncinsa a Musulunci

4. Sauya kayan NYSC zuwa Adire

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana duba yiwuwar sauya kayan kaki na masu yi wa kasa hidima (NYSC) zuwa kayan Adire a matsayin wani bangare na sauye-sauyen da ake shirin aiwatarwa a shirin.

An dauko batun sauya kayan NYSC
Matasa da suka kammala NYSC da hoton wasu sanye da kayan adire Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ministan Raya Matasa, Ayodele Olawande, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Channels inda ya ce hakan zai bunkasa amfani da kayayyakin cikin gida.

Bayan yan Najeriya sun yi ca a kan batun kuma tuni gwamnatin tarayya ta yi karin haske cewa ba a yanke hukunci kan sauya kayan ba, illa dai an yi amfani da batun Adire ne a matsayin misali yayin bayanin sauye-sauyen da ake son yi.

5.Nasarar ADC a kotu

A ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli, 2026 Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da halascin shugabancin jam'iyyar ADC karkashin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark.

Kotu ta tabbatar da nasarar David Mark a shari'ar ADC
Shugaban jam'iyyar ADC David Mark Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa kotun ta yi watsi da karar da dan Majalisar Wakilai, Leke Abejide, ya shigar, tana mai cewa ba ta da hurumin sauraron batun saboda ya shafi harkokin cikin gida na jam'iyyar siyasa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa masu koyon karatun Alkur'ani wuta a Bauchi

Daily Post ta wallafa cewa Mai shari'a Musa Liman ya kuma bayyana cewa Abejide bai gabatar da hujjar da ta nuna an take masa wata hakki ba, saboda haka ba shi da damar shigar da karar.

6. Janye dakaraun Amurka

A wani muhimmin ci gaba, rundunar sojin Amurka mai kula da nahiyar Afirka (AFRICOM) ta sanar da janye mafi yawan dakarunta da aka tura Najeriya domin tallafawa ayyukan yaki da ta'addanci.

Premium Times ta kawo labarin cewa Kwamandan AFRICOM, Dagvin Anderson, ya ce duk da janyewar dakarun, Amurka za ta ci gaba da bai wa Najeriya hadin kai ta fuskar musayar bayanan sirri da sauran hanyoyin hadin gwiwar tsaro.

Wasu daga cikin dakarun Amurka sun bar Najeriya
Shugaban kasar Amurka Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Tun a watan Fabrairu, 2026 ne aka tura karamin rukuni na sojojin Amurka zuwa Arewa maso Gabashin Najeriya bayan cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatocin kasashen biyu.

A lokacin, gwamnatin Amurka ta bayyana cewa manufar tura dakarun ita ce karfafa yaki da kungiyoyin ta'addanci, yayin da hukumomin tsaron Najeriya suka tabbatar da cewa sojojin Amurka ba za su shiga kai tsaye a fagen daga ba.

Tinubu ya rada wa matarsa sabon suna

A baya, mun kawo labarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi wa uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu, lakabi da wani suna cikin barkwanci yayin wani taro bayan kalaman da ta yi game da mata su kama kananan sana'o'i

Kara karanta wannan

Iyayen daliban da aka sace sun rusa kuka bayan ziyarar tawagar Zulum

Lakabin ya biyo bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan kalaman uwargidan shugaban ƙasar na ƙarfafa mata su fara sayar da kosai, inda yan Najeriya ke ganin kamar akwai izgilanci da cin fuska a lamarin.

Daga baya Oluremi Tinubu ta fayyace cewa shirin tallafin gwamnati ya shafi masu sana'o'i daban-daban, ba masu sayar da kosai kaɗai ba, kuma tana nan a kan bakarta na karfafa wa irin masu wadannan sana'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng