Gwamnati Ta Kashe N500m a Kare Martabar Najeriya kan Zargin Gallazawa Kiristoci
- Rahotanni sun bankado yadda gwamnatin Tarayya ta kashe Naira miliyan 500 domin yaƙi da zargin gallazawa Kiristoci a Najeriya
- Wannan na zuwa ne kuma bayan an rattaba hannu a kan yarjejeniyar $9m da kamfanin kamun kafa na Amurka domin kare martabar Najeriya
- Bayan Amurka da Donald Trump su ka sako Najeriya a gaba da zargin an bari ana kashe kiristoci da gayya da niyyar kisan kare dangi aka kasar ta shiga damuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rahotannin dandalin bibiyar kashe kuɗaɗen gwamnati na GovSpend sun nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira miliyan 500 a shekarar 2025 don gyara tunanin jama'a kan batun kashe kiristoci.
Bayanan sun nuna cewa an fitar da kuɗin ne domin aikin da aka bayyana a matsayin yaƙi da haɗaɗɗiyar farfagandar ƙasashen Yamma kan zargin gwamnatin Najeriya da gallazawa Kiristoci.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa an biya kuɗin ne a ranar 19 ga Disamba, 2025, ta hannun Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa.
Yadda gwamnati ke fafutuka kan kiristoci
Matakin ya nuna yadda gwamnati ta ƙara zuba jari wajen inganta sadarwa da kare martabar Najeriya yayin da ake ci gaba da nuna damuwa daga ƙasashen waje kan matsalar tsaro da kuma zarge-zargen cin zarafin 'yancin addini.
A wannan shekarar ce kuma gwamnatin ta ɗauki wani kamfanin kamun kafa na Amurka, DCI Group, ƙarƙashin kwangilar $9m domin ƙarfafa hulɗa da jami'an gwamnatin Amurka kan batun hare-haren da ake zargin ana kai wa kiristoci.
Takardun da aka shigar ƙarƙashin dokar Foreign Agents Registration Act (FARA) sun nuna cewa kamfanin lauyoyi na Aster Legal da ke Kaduna ne ya ɗauki DCI Group a madadin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu.
Yadda aka kulla yarjejeniya a gwamnati
Yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a ranar 18 ga Disamba, 2025, ta tanadi cewa kamfanin zai taimaka wajen bayyana matakan da Najeriya ke ɗauka na kare al'ummomin kiristoci.
Haka kuma an tanadi a tabbatar da ci gaba da samun goyon bayan Amurka wajen yaƙi da Boko Haram, ISWAP da sauran ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi.

Source: Facebook
Bisa yarjejeniyar, gwamnatin ta amince za ta riƙa biyan kamfanin Dala 750,000 duk wata, wanda zai kai $9m cikin shekara guda idan aka ci gaba da kwangilar.
Kwangilar ta biyo bayan yadda gwamnatin Amurka ta sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da take haƙƙin 'yancin addini, wato CPC, a watan Oktoban 2025.
An yi magana kan kisan kiristoci
A wani labarin, mun wallafa cewa Sanata Ted Cruz na Amurka ya zargi wasu manyan jami’an gwamnatin Najeriya da haɗa baki wajen kisan gilla ga kiristoci a sassan ƙasar da gayya da kuma niyyar kisan kare dangi.
Sanata Ted Cruz ya ce tun daga 2009, an kashe kiristoci sama da 50,000 tare da ruguza majami'u da makarantu 20,000 saboda tsatsauran ra'ayi, wanda ake ganin cewa gwamnati ta yi biris da lamarin.
Ya bayyana cewa ya taɓa gana wa da manyan jami'an tsaron Najeriya a bara inda suka yi alkawarin kawo ƙarshen tashin hankalin, amma a cewarsa, har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Asali: Legit.ng


