A Karshe, Amurka Ta Janye Sojojinta daga Najeriya, Ta Sabunta Salon Alakarsu
- Kasar Amurka ta janye yawancin dakarunta daga yaƙi da ta'addanci a Najeriya da Tafkin Chadi bayan tabbatar da cimma nasara
- Janar Dagvin Anderson ya ce haɗin gwiwar bayanan sirri tsakanin Amurka da Najeriya ya taimaka wajen kashe shugaban ISIS
- Amurka ta ce haɗin gwiwar ƙasashen Afirka wajen musayar bayanan sirri zai taimaka wajen yaƙar ta'addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Amurka ta janye mafi yawan dakarunta da aka tura Najeriya domin aikin haɗin gwiwa na yaƙi da ta'addanci a yankin Tafkin Chadi.
Sai dai ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da musayar bayanan sirri da sauran haɗin gwiwar tsaro da Najeriya.

Source: Getty Images
Kwamandan Rundunar Sojin Sama ta Amurka a Turai da Afirka, Janar Dagvin R.M. Anderson, ne ya bayyana hakan yayin wani taro, cewar Punch.
Amurka za ta sabunta alaka da Najeriya
Ya bayyana cewa aikin sojan da aka gudanar ya ƙare, kuma yawancin sojojin Amurka da suka shiga aikin sun bar Najeriya bayan kammala aikinsu cikin nasara.
Sai dai ya ce gwamnatin Amurka za ta ci gaba da tallafa wa Najeriya ta hanyar musayar bayanan sirri, bisa buƙatar gwamnatin Najeriya domin ci gaba da yaƙi da ta'addanci.
Anderson ya ce aikin da aka gudanar a yankin Tafkin Chadi bai amfani ƙasashen yankin kaɗai ba, har ma ya taimaka wajen raunana cibiyar sadarwar ƙungiyar ISIS a duniya baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa janye dakarun ba yana nufin kawo ƙarshen haɗin gwiwa ba, domin za a ci gaba da samar da bayanan sirri da sauran ƙwarewar da Najeriya ke buƙata.

Source: Facebook
Yabon da Najeriya ta samu daga Anderson
Janar ɗin ya bayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai ƙarfi da rundunar soji mai nagarta, yana mai cewa haɗin gwiwar ƙasashen biyu ya samar da manyan nasarori wajen yaƙar ƙungiyar ISIS.
A cewarsa, haɗuwar bayanan sirrin Amurka da ƙoƙarin sojojin Najeriya ne ya kai ga nasarar kai farmaki kan mataimakin shugaban ƙungiyar ISIS na duniya.
Ya ce Amurka ta ba Najeriya ƙwarewa da dabarun da ta koya tsawon shekaru wajen yaƙi da ta'addanci, lamarin da ya taimaka wajen cimma wannan nasara ta haɗin gwiwa.
Anderson ya bayyana cewa wannan nasarar ta nuna muhimmancin musayar bayanan sirri fiye da dogaro da kasancewar sojojin ƙasashen waje na dogon lokaci.
Ya ce Amurka za ta ci gaba da bai wa ƙawayenta irin ƙwarewar da take da ita domin su ƙara ƙarfi wajen tunkarar ƙungiyoyin ta'addanci, cewar Vanguard.
Har ila yau, ya buƙaci ƙasashen Afirka su ƙarfafa haɗin gwiwa wajen musayar bayanan sirri domin yaƙar ta'addanci, safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifukan da ke ƙetare iyakoki.
Alwashin da sojojin Amurka da Najeirya suka yi
An ji cewa sojojin Najeriya da na Amurka sun yi magana kan hadakar da suke yi saboda yaki da ta'addanci a fadin kasar baki daya.
Kasashen biyu sun sake jaddada aniyarsu ta karfafa hadin gwiwa wajen yaki ta hanyar musayar bayanan sirri da horaswa.
Hedikwatar Tsaro ta bayyana cewa dakarun kasashen biyu sun gudanar da hare-haren hadin gwiwa kan 'yan ta'adda.
Asali: Legit.ng

