'Yan Bindiga Sun Bindige Kwamandan Jami'an Tsaro da Wasu Mata

'Yan Bindiga Sun Bindige Kwamandan Jami'an Tsaro da Wasu Mata

  • ‘Yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne sun kashe kwamandan OSPAC na yankin Omoku da mata uku a harin da suka kai a kan titin Oba
  • Harin ya jefa mazauna Omoku cikin firgici, inda suka tsere domin tsira yayin da ‘yan kasuwa suka rufe shagunansu
  • OSPAC da ‘yan sanda sun yi kira ga mazauna garin su kwantar da hankalinsu tare da taimakawa wajen gano wadanda suka aikata laifin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Rivers - ‘Yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne sun kashe Kwamandan 'yan sa-kai na OSPAC na yankin Omoku, Ozomela Stephen Nwaocha a jihar Rivers.

'Yan bindigan sun kuma kashe wasu mata uku a wani hari da suka kai a kan titin Oba Road da ke Omoku, karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni ta jihar Rivers.

'Yan bindiga sun yi barna a Rivers
Taswirar jihar Rivers, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, 20 ga watan Yulin 2026 yayin da kwamandan kungiyar sa-kai ke zaune yana hutawa tare da ‘yar uwarsa da kawarta a kusa da gidansa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An gano jami'ar bogi da ta tara dalibai a Najeriya

Harin ya jefa al’ummar garin cikin firgici, inda mazauna yankin suka rika gudu domin tsira yayin da ‘yan kasuwa suka rufe shagunansu cikin gaggawa saboda fargabar sake barkewar tashin hankali.

Mutane na tsoron komawar zamanin Don Wanie

Ko da yake babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, mazauna yankin sun ce kisan kwamandan OSPAC na iya zama alamar sake dawowar kashe-kashen gilla da suka addabi yankin kafin kafa rundunar tsaron yankin.

Mazauna garin sun kuma ce an kashe jami’an OSPAC da dama a ‘yan kwanakin nan, lamarin da ya kara jefa su cikin fargabar yiwuwar komawar zamanin “Don Wanie” a yankin

OSPAC ta tabbatar da harin

Jami’in hulda da jama’a na OSPAC a jihar Rivers, Kwamared Nkem Godknows, ya tabbatar da faruwar lamarin

Ya ce ‘yan bindigar sun kai wa kwamandan hari ne yayin da yake hutawa tare da ‘yar uwarsa da kawarta a kusa da gidansa.

“Lamarin ya faru ne bayan ‘yan mintoci kadan da karfe 5:00 na yamma. Kwamandanmu yana tare da ‘yar uwarsa da kawarta, suna zaune a unguwarsu, lokacin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka zo suka harbe shi har lahira."

Kara karanta wannan

Tinubu ya kaddamar da manyan ayyukan tallafawa talakawa

“Mata uku sun mutu nan take, yayin da wasu mutane biyu suka samu raunukan harbin bindiga kuma a halin yanzu ana kula da su a asibiti. An sanar da ‘yan sanda nan take kuma muka kai rahoton lamarin ba tare da bata lokaci ba."
“Ina kira ga mutanen Omoku da su kwantar da hankalinsu, su zauna lafiya, su kuma ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Kada kowa ya firgita. Da yardar Allah, OSPAC tare da sauran hukumomin tsaro za su gano bakin zaren wannan lamari.”

- Nkem Godknows

‘Yan sanda sun yi alkawari

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Rivers, ASP Agabe Blessing Kaborlo, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce za a gurfanar da wadanda suka aikata kisan a gaban hukuma.

Ya bukaci jama’ar da ke da muhimman bayanai da za su taimaka wa binciken su tuntubi ‘yan sanda.

'Yan bindiga sun yi barna a Rivers
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan bindiga sun kashe mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a wasu kauyukan jihar Sokoto.

'Yan bindigan sun hallaka mutane bayan da suka bude wuta kan mai uwa da wabi a hare-haren na ta'addanci da suka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng