Matar Aure Ta Kwarawa Kishiyarta Mai Ciki Ruwan Zafi, Ta Haihu Dan Ya Mutu

Matar Aure Ta Kwarawa Kishiyarta Mai Ciki Ruwan Zafi, Ta Haihu Dan Ya Mutu

  • Rundunar 'yan sandan Bauchi ta kama wata mata bisa zargin kwarawa kishiyarta mai juna biyu ruwan zafi yayin wata takaddama a gida
  • Bayan harin, matar ta haihu a asibiti amma jaririn ya rasu sakamakon munanan ƙonewar da ya samu, yayin da ita kuma ke ci gaba da jinya
  • 'Yan sanda sun ce wadda ake zargin ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi, kuma za a miƙa shari'ar zuwa sashen binciken manyan laifuffuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi – Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da kama wata mata mai suna Rabi Abubakar bisa zargin kwarawa kishiyarta mai juna biyu ruwan zafi a ƙauyen Daba.

Ana zargin lamarin ya faru ne sakamakon wata takaddama da ta ɓarke a tsakanin matan biyu, wanda daga bisani ya kai ga jikkata matar mai juna biyu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun birkita kauyen Sokoto da harbi, sun sace sama da mutum 50

Taswirar jihar Bauchi
Taswirar jihar Bauchi a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Punch ta rahoto cewa bayan an kai matar asibiti domin ceto rayuwarta, ta haihu amma jaririn da ta haifa ya rasu saboda munanan ƙonewar da ya samu.

Yadda aka kona matar aure

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan Bauchi, CSP Nafiu Habib, ya fitar a Facebook, ya ce ofishin 'yan sanda na Dabe ne ya kai rahoton lamarin ga rundunar a ranar 22 ga Yulin 2026.

Sanarwar ta ce ana zargin Rabi Abubakar ta zuba wa kishiyarta mai shekaru 30 ruwan zafi ne da misalin ƙarfe 7:30 na safiyar ranar 17 ga Yuli yayin wani saɓani da ya taso a gida.

Bayan harin, an garzaya da matar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi domin samun kulawar likitoci.

Sufeton 'yan sanda na bayani.
Shugaban 'yan sandan Najeriya, Tunji Disu. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Jaririn ya rasu bayan haihuwa

'Yan sandan sun bayyana cewa matar na ɗauke da tsohon ciki lokacin da aka aka kwarara mata zuwan zafin.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya bayyana matsayar Kano kan kafa 'yan sandan jiha

A ranar 19 ga Yuli ta haifi jariri namiji, amma ya samu munanan raunukan ƙonewa kuma ya rasu a ranar da aka haife shi.

Sanarwar 'yan sanda ta ƙara da cewa matar na ci gaba da samun sauƙi a asibiti kuma tana samun sauki.

Matakin da 'yan sanda suka ɗauka

Rundunar ta ce bayan samun rahoton, jami'anta sun ziyarci wurin da lamarin ya faru tare da cafke wacce ake zargi.

A cewar kakakin rundunar, yayin binciken farko matar ta amsa laifin da ake zarginta da aikatawa.

An ce tana tsare a hannun 'yan sanda, kuma za a miƙa shari'ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) na jihar Bauchi domin ci gaba da bincike da gurfanar da ita a gaban kotu.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi Allah wadai da lamarin, yana mai kira ga jama'a da su rika warware saɓani cikin lumana tare da kai rahoton rikicin cikin gida ga jami'an tsaro.

Jarumar fim ta nemi taimako

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Ngozi Nwosu, ta roƙi 'yan Najeriya da masoyanta su taimaka mata.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An gano jami'ar bogi da ta tara dalibai a Najeriya

Jarumar ta bayyana cewa ta shafe makonni uku tana kwance a asibiti, kuma ana shirin yi mata manyan tiyata uku domin ceto rayuwarta.

Ngozi Nwosu ta bayyana hakan ne cikin wani bidiyo, inda ta ce halin da take ciki ya fi ƙarfinta kuma tana buƙatar taimakon jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng