Saudiyya Ta Yi wa Tinubu Gayyata Ta Musamman, Asiwaju zai Je Taron Duniya Riyadh
- Shugaba Bola Tinubu ya karɓi gayyata daga Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman domin halartar babban taron zuba jari na FII
- Jakadan Saudiyya a Najeriya ne ya miƙa gayyatar ga shugaban ƙasa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a madadin Yariman Saudiyya
- Tinubu ya yabawa dangantakar Najeriya da Saudiyya, yana mai cewa haɗin gwiwar ƙasashen biyu na ci gaba da ƙarfafa a fannoni daban-daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi gayyata daga Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman bin Abdulaziz, domin halartar taron zuba jari na FII karo na 10.
Taron wanda ake sa ran gudanarwa a birnin Riyadh a watan Oktoban 2026 na ɗaya daga cikin manyan tarukan zuba jari da tattalin arziki na duniya.

Source: Twitter
Punch ta rahoto cewa Jakadan Saudiyya a Najeriya, Yousef Albalawi, ne ya miƙa gayyatar ga Shugaba Tinubu a ranar Juma'a yayin wata ganawa da aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Yadda aka miƙa gayyatar ga Tinubu
A cewar wani saƙo da Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Najeriya ya wallafa a shafinsa na X, jakadan ya miƙa gayyatar ne a madadin Yarima Mohammed bin Salman.
Sanarwar ta bayyana cewa an gayyaci Shugaba Tinubu ne domin halartar babban taron zuba jari na FII, wanda ke tattaro shugabannin ƙasashe, masu zuba jari da manyan 'yan kasuwa daga sassa daban-daban na duniya.
Martanin Tinubu ga Saudi
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa yana matuƙar godiya da wannan gayyata, tare da yaba dangantakar da ke tsakanin Tarayyar Najeriya da Masarautar Saudiyya.
Ya ce haɗin gwiwar ƙasashen biyu na ci gaba da bunƙasa a fannoni daban-daban, yana mai jaddada cewa dangantakar na da muhimmanci wajen haɓaka ci gaban tattalin arziki da zuba jari.
Sanarwar ta kuma ce shugaban ya sake tabbatar da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Abin da ya kamata a sani game da taron FII
Taron FII, wanda aka fi sani da "Davos in the Desert", shi ne babban taron zuba jari na Saudiyya da ake gudanarwa duk shekara.
Cibiyar FIII mai zaman kanta ce ke shirya taron a Riyadh domin haɗa shugabannin ƙasashe, masu saka hannun jari, kamfanoni, masu kirkire-kirkire da masu tsara manufofi.
An ƙaddamar da taron a shekarar 2017 a matsayin wani ɓangare na habaka Saudiyya, kuma bana zai cika shekara 10 da kafuwarsa.
Ana sa ran taron na bana zai mayar da hankali kan batutuwa kamar fasahar AI, makamashi, sauyin yanayi, kiwon lafiya, gine-gine, masana'antu da hanyoyin bunƙasa tattalin arzikin duniya.
Trump ya yaba wa Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaba Donald Trump ya yabawa shugaba Bola Tinubu kan matakan da yake ɗauka wajen yaƙi da ta'addanci da matsalar tsaro a Najeriya.
Trump ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aika wa Tinubu, inda ya ce ya nuna jagoranci mai ƙarfi wajen tunkarar hare-haren 'yan ta'adda da ke addabar wasu sassan ƙasar.
Haka kuma, Trump ya sake tabbatar da cewa Amurka za ta ci gaba da tallafa wa Najeriya wajen yaƙi da ta'addanci da ƙarfafa tsaro.
Asali: Legit.ng

