Iyayen Daliban da aka Sace Sun Rusa Kuka bayan Ziyarar Tawagar Zulum
- Gwamna Babagana Umara Zulum, ya tura tawaga mai karfi zuwa garin Lassa bayan harin da 'yan ISWAP suka kai makaranta suka sace dalibai
- Gwamnatin Borno ta ce tana aiki ba dare ba rana tare da hukumomi da sauran shugabanni domin ceto ɗalibai da malaman da aka sace
- A yayin ziyarar, jihar Borno ta yanke shawarar rufe makarantu a yankunan Dille, Lassa da Chul kafin lamura su daidaita a wuraren
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya tura wata babbar tawaga zuwa garin Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira/Uba bayan harin da 'yan ta'adda suka kai makarantar sakandare.
Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha, Lawan Abba Wakilbe, ne ya jagoranci tawagar, wadda ta ƙunshi kwamishinan harkokin gwamnati, Hon. Samaila Satumari da babbar sakatariyar ma'aikatar muhalli, Dr Juliana Bitrus.

Source: Facebook
A sakon da hadimin Zulum, Dauda Iliya ya wallafa a Facebook, ya ce tawagar ta haɗa da mai ba gwamna shawara, Emmanuel Yerima; wakilin NUT, Kwamared Suleiman Bello Maina; da sauran manyan jami'an gwamnati.
An gana da iyayen dalibai
Da isarsu Lassa, tawagar ta gana da iyayen ɗaliban da abin ya shafa, inda da dama daga cikinsu suka bayyana damuwa matuƙa kan lafiyar da kuma inda 'ya'yansu suke.
A hotunan da aka wallafa yayin ziyarar, iyayen dalibai maza da mata sun rusa kuka, lamarin da ke nuna halin damuwa da suka shiga.
Da yake jawabi ga iyayen, shugaban tawagar, Wakilbe, ya isar da saƙon jaje na gwamna Babagana Zulum tare da tabbatar masu cewa gwamnatin jihar na aiki kafaɗa da kafaɗa da jami'an tsaro don ceto daliban.
Tribune ta rahoto ya ce:
“A madadin mai girma Gwamna, Farfesa Babagana Umara Zulum, muna miƙa ta'aziyyarmu kan wannan mummunan lamari. Ina tabbatar muku cewa jami'an tsaro, gwamnati, shugabannin al'umma da sauran masu ruwa da tsaki na ci gaba da ƙoƙari domin gano tare da dawo da ɗalibai da ma'aikatan da aka sace cikin aminci,”
Makarantar da aka sace dalibai
Daga nan tawagar ta wuce makarantar sakandaren 'Yan Mata ta gwamnati da ke Lassa, inda kwamishinan ya jagoranci wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki.
Bayan doguwar tattaunawa, taron ya yanke shawarar rufe dukkan makarantu na ɗan lokaci a al'ummomin Dille, Lassa da Chul a matsayin matakin kariya ta fuskar tsaro.

Source: Facebook
Adadin daliban da aka sace
A yayin taron, Shugaban Ƙaramar Hukumar Askira/Uba, Hon. Mada Saidu, ya miƙa wa tawagar jerin sunayen waɗanda harin ya shafa.
Bisa rahoton da aka gabatar, mutum 39 daga Makarantar sakandaren gwamnati da ke Lassa ne harin ya shafa, waɗanda suka haɗa da malamai uku da ɗalibai 36.
Rahoton ya kuma nuna cewa cikin ɗaliban 36 da suka ɓace akwai mata 25 da maza 11, waɗanda suka fito daga azuzuwan SS1, SS2 da SS3.
An ceto wasu dalibai a Borno
A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun Najeriya sun kai dauki cikin gaggawa bayan 'yan ta'addan ISWAP sun kai hari makaranta a Borno.
Bayan musayar wuta da 'yan ta'addan da kai masu farmaki ta sama, sojojin Najeriya sun yi nasarar ceto wasu daga cikin daliban da aka sace.
Jihar Borno dai ta shafe tsawon shekaru tana fuskantar hare-haren 'yan ta'adda, lamarin da ya kai ga sace dalibai a makarantu daban-daban.
Asali: Legit.ng


