Peter Obi: An Ji Bayanin Abin da Ya Faru da Dan Takarar NDC Ya Tattauna da Jakandan Birtaniya
- Dan takarar jam'iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi, ya bayyana abin da ya tattauna da babban jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr Richard Montgomery
- Tattaunawar tasu ta mayar da hankali kan dimokuradiyyar Najeriya, tattalin arziki da karfafa hukumomi gabanin zabuka masu zuwa
- Obi ya ce ya gode wa jakadan bisa gudunmawarsa wajen karfafa alakar Najeriya da Birtaniya yayin da yake shirin kammala aikinsa a Najeriya a wata mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dan takarar jam'iyyar NDC a zaben shugaban kasa na 2027, Peter Obi, ya bayyana cewa ya gana da babban jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr Richard Montgomery.
Peter Obi ya bayyana cewa sun tattauna kan dimokuradiyyar Najeriya, tattalin arziki da muhimmancin karfafa hukumomi gabanin zabuka masu zuwa.

Source: Twitter
Obi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 23 ga watan Yulin 2026 a shafinsa na X.
Ya ce tattaunawar tasu ta shafi halin da dimokuradiyyar Najeriya ke ciki, kalubalen tattalin arziki da kuma muhimmancin gudanar da sahihan zabuka.
Abin da Obi ya tattauna da Montgomery
"A yau, na gana da babban jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr Richard Montgomery. Mun yi tattaunawa mai zurfi kan halin da dimokuradiyyarmu take ciki, tattalin arziki, muhimmancin karfafa hukumominmu da kuma bukatar tabbatar da cewa zabukanmu sun ci gaba da kasancewa cikin 'yanci, adalci, sahihanci tare da bayyana ainihin muradin al'ummar Najeriya," in ji shi
Obi ya kuma gode wa jakadan Birtaniya bisa gudunmawar da ya bayar wajen karfafa alakar Najeriya da Birtaniya yayin da jami'in diflomasiyyar ke shirin kammala aikinsa a Najeriya a wata mai zuwa.
Obi ya gode wa jakadan Birtaniya
"Yayin da Dr Montgomery ke shirin kammala aikinsa na diflomasiyya a Najeriya a wata mai zuwa, na gode masa bisa hidimar da ya yi da kuma rawar da ya taka wajen karfafa dadaddiyar alakar Najeriya da Birtaniya. Lokacinsa a Najeriya ya kasance na hadin gwiwa mai ma'ana da goyon baya ga ci gaban dimokuradiyya da tattalin arzikinmu," in ji Obi
Obi ya yi wa jakadan fatan samun nasara a sabon aikin da zai koma, tare da bayyana fatansa cewa alakar kasashen biyu za ta ci gaba da bunkasa.
Ya kara da cewa:
"Na yi masa fatan alheri yayin da yake shirin komawa sabon aiki, sannan na gode masa bisa abota da hadin gwiwar da ya nuna wa Najeriya a tsawon lokacin da ya yi a nan. Ina fatan ganin karfin alakar kasashenmu biyu na ci gaba da bunkasa.

Source: Twitter
Ganawar ta zo ne kwana guda bayan Obi ya gana da Jakadan Switzerland a Najeriya, Patrick Egloff, inda suka tattauna kan muhimman abubuwan da Najeriya ke bukata domin ci gaba, musamman ilimi, kiwon lafiya da rage talauci.
Peter Obi ya hango nasara a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC) a zaɓen 2027, Peter Obi, ya bayyana cewa ya na da yakinin zai yi nasara.
Peter Obi ya bayyana cewa zaɓen ba fafatawa ce ta siyasa tsakaninsa da gwamnati mai ci ba, illa dai tsakanin ‘yan Najeriya da gwamnatin ƙasar.
Asali: Legit.ng

