Tinubu Rada wa Matarsa Oluremi Sabon Suna bayan Kalamanta kan Tallar Kosai
- Shugaba Bola Tinubu ya yi wa uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu, lakabi da wani suna cikin barkwanci yayin wani taro
- Lakabin ya biyo bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan kalaman uwargidan shugaban ƙasar na ƙarfafa mata su fara sayar da kosai
- Daga baya Oluremi Tinubu ta fayyace cewa shirin tallafin gwamnati ya shafi masu sana'o'i daban-daban, ba masu sayar da kosai kaɗai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya kira uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu, da wani suna bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan kalamanta.
Tinubu ya yi mata lakabi da "Iya Alakara" cikin barkwanci, yana nuni da maganganun da suka biyo bayan kalamanta kan ƙananan sana'o'i.

Source: Twitter
Shugaban ya yi wannan furuci ne yayin jawabinsa a liyafar cin abinci da aka shirya wa mambobin Ƙungiyar 'Yan Jaridun Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, wanda TVC News ta yada bidiyon.
Lakabin da Tinubu ya ba Oluremi
Bayan ya gaisa da mahalarta taron, shugaban ya juya ga uwargidansa yana cewa, "Barka da yamma, uwargidata, Uwargidan Shugaban Ƙasa, Iya Alakara."
Wannan kalami ya jawo dariya da martani daga waɗanda suka halarci taron duba da irin salon yadda Tinubu ya yi maganar.
Lakabin ya zo ne bayan wasu makonni da Uwargidan Shugaban Ƙasa ta shawarci matan Najeriya su rungumi ƙananan sana'o'i kamar sayar da kosai, gasasshen masara da kuli-kuli.
Ta bayyana cewa irin waɗannan sana'o'i ba sa buƙatar kuɗi masu yawa domin fara su, a ƙarƙashin shirin Renewed Hope Initiative.

Source: Facebook
Kalaman Oluremi da suka jawo maganganu
Kalaman nata sun jawo muhawara sosai a shafukan sada zumunta, inda wasu 'yan Najeriya suka soki furucin suna cewa bai dace da halin matsin tattalin arzikin da jama'a ke ciki ba.
Sai dai daga baya Uwargidan Shugaban Ƙasa ta fayyace cewa shirin tallafa wa masu sana'o'i bai taƙaitu ga masu sayar da kosai kaɗai ba.
Da take mayar da martani kan suka da aka yi mata, ta ce gwamnatin tarayya ta ba gwamnatin Jigawa tallafin naira miliyan 100 domin ƙarfafa ƙananan 'yan kasuwa 2,000.
Ta ce mutane sun fi mayar da hankali kan batun kosai, alhali shirin ya haɗa da masu sayar da tumatir, barkono, kayan lambu da gasasshen ayaba.
Oluremi Tinubu ta ce gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa waɗannan ƙananan 'yan kasuwa domin bunƙasa jarinsu da tabbatar da dorewar sana'o'insu.
Fadar shugaban kasa ta kare kalaman Oluremi
Mun ba ku labarin cewa Fadar Shugaban Kasa ta kare kananan sana'o'i, tana cewa akwai mutunci a cikinsu bayan kalaman Sanata Oluremi Tinubu.
Mai ba shugaban kasa shawara, Sunday Dare, ya ce an fahimci kalaman Uwargidan Shugaban Kasa ba daidai ba.
Fadar Shugaban Kasa ta ce sana'o'in akara, masara da kuli-kuli na samar wa miliyoyin 'yan Najeriya abin dogaro da kuma tallafa wa tattalin arziki.
Asali: Legit.ng

