Idon Trump Ya Koma kan Kadarorin Iran da ke Amurka, Ya Fara Kai Masu Barazana

Idon Trump Ya Koma kan Kadarorin Iran da ke Amurka, Ya Fara Kai Masu Barazana

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya fara magana a kan yiwuwar amfani da kadarorin Daular Musulunci ta Iran da aka daskarar a bankunan kasarsa
  • Donald Trump, wanda da kasarsa da Isra'ila su ka hada hannu wurin fara kai wa Iran hari a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2026 ya ce za a yi amfani da kudin Iran
  • Tuni Iran ta soki matakin, tana mai gargadin cewa zai iya haifar da rikici da kuma jefa sauran kasashe da ke da dukiya a Amuka a cikin barazana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

USA – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi amfani da kuɗaɗen Iran da Amurka ta daskarar a kasarsa.

Ya yi barazanar amfani da kudaden domin biyan duk wata diyya da ta shafi lalacewar jiragen ruwa, kayayyaki ko wasu asarar da ake dangantawa da hare haren da Iran ko ƙawayenta suka haddasa.

Kara karanta wannan

Trump ya lallaba ya tura bukatar tsagaita wuta Iran ta Iraq, Tehran ta yi martani

Amurka ta farra barazana ga dukiyoyin Iran
Shugaban kasar Amurka Donald Trump, Mojtaba Khamnei na Iran Hoto: Donald J Trump, Imam Sayyid Mojtaba Khamnei
Source: Getty Images

BBC News ta kawo labarin cewa kalaman na Trump sun zo ne yayin da rundunar sojin Amurka ta sanar da kai hare hare kan Iran a daren 13 a jere.

Trump ya yi barazana ga Iran

Bloomberg ta ruwaito cewa Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran sun ce mutane huɗu sun mutu yayin da wasu biyar suka jikkata sakamakon sabbin hare haren.

A cewar rundunar Amurka, CENTCOM, an kai hare-haren ne domin rage ƙarfin Iran na barazana ga zirga zirgar jiragen ruwa a yankin.

Ta ce an kai hari kan cibiyoyin umarnin soji, wuraren adana jiragen sama marasa matuƙa, hanyoyin sadarwa, cibiyoyin sa ido a gabar teku da sauran kayan aikin ruwa na Iran.

Sababbin hare haren sun biyo bayan ikirarin mayaƙan Houthi na Yemen, waɗanda Iran ke marawa baya, cewa sun kai hari kan wasu tankokin mai biyu na Saudiyya a Tekun Bahar Maliya.

Martanin Iran ga Trump

Kara karanta wannan

An kashe iyalan fasto a Filato, Amurka ta yi gargadi kwana 1 bayan yabon Tinubu

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi kakkausar suka ga kalaman Trump, yana mai cewa wannan mataki na iya zama wata haɗariyar kafa sabuwar al'ada.

Ya rubuta cewa:

"Waɗanda ke murna ko cin moriyar irin waɗannan kuɗaɗe su tuna cewa idan gwamnatoci suka fara halasta ƙwace kadarorin wasu ƙasashe, kadarorin kowa ba za su ƙara zama cikin aminci ba."
Iran tagargadi Amurka kan taba dukiyar ta
Shugaban kasar Iran, Masoud Pazeskian Hoto: Iran News
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa:

"Rikicin da zai biyo baya ba zai kasance mai kyau ko zaman lafiya ba."

Yayin da rikicin ke ƙara ƙamari, farashin ɗanyen mai ya haura Dala 100 kan kowace ganga, matakin da bai kai ba tun watan Mayu.

Trump ya tura Iraqi zuwa Iran

A baya, mun wallafa cewa Iran ta ƙi amincewa da wata sabuwar shawarar tsagaita wuta da Amurka ta aike mata ta hannun Firaministan Iraki, Ali al-Zaidi yayin da ta ke ci gaba da kai mata hari.

Rahotanni sun nuna cewa Tehran ta ce shawarwarin ba su magance rikicin da ya shafi ikon sarrafa mashigar ruwa ta Hormuz ba, saboda haka ba abu ne da za a iya amincewa da shi ba a wannan lokaci.

Yayin da rikice-rikice da yaki ke ci gaba a Gabas ta Tsakiya, sojojin Amurka sun kai hare-hare kan Iran na dare na 13 a jere yayin da Amurk ke ci gaba da yi wa Iran da magoya bayan ta barazana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng