An Bude Shafin ba 'Yan Najeriya Tallafin Karatu na Naira Miliyan 25 da Kwamfuta

An Bude Shafin ba 'Yan Najeriya Tallafin Karatu na Naira Miliyan 25 da Kwamfuta

  • Tunde Onakoya tare da wasu abokan hulɗarsa sun ƙaddamar da tallafin karatu na N250m domin matasa masu yi wa ƙasa hidima da sabbin waɗanda suka kammala NYSC
  • Masu cin gajiyar shirin za su samu tallafin karatu na N160,000, damar samun horo kan fasahar zamani, aikin yi da kuma kwamfutar tafi-da-gidanka ga waɗanda aka zaɓa
  • Masu shirya shirin sun bayyana matakan da masu sha'awa za su bi wajen neman tallafin domin samun damar shiga shirye-shiryen AltSchool Africa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Wanda ya kafa ƙungiyar Chess in Slums Africa, Tunde Onakoya, ya haɗa hannu da wanda ya kafa Jobs59, Sam Otigba, da kuma wanda ya kafa AltSchool Africa, HackSultan, wajen ƙaddamar da tallafin karatu na Naira miliyan 250.

Shirin na da nufin bai wa matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da waɗanda suka kammala hidimar ƙasa damar koyon dabarun fasahar zamani da ake buƙata a duniyar yau.

Kara karanta wannan

An samu matsala a kotu kan sharudan belin shugaban Miyetti Allah, Bodejo

Na'ura mai kwakwalwa
Wayar hannu da na'ura mai kwakwalwa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Punch ta rahoto cewa masu cin gajiyar shirin za su samu tallafin karatu na N160,000, da damar samun horo, jagoranci kan sana'a, guraben aikin horaswa da kuma kwamfutocin tafi-da-gidanka ga wasu daga cikinsu.

Wadanda za a ba tallafin

Masu shirya shirin sun bayyana cewa kofar tallafin a buɗe take ga masu yi wa ƙasa hidima, waɗanda ke shirin fara NYSC da kuma waɗanda suka kammala hidimar ƙasa kwanan nan.

A cewarsu, an ƙirƙiri shirin ne domin taimaka wa matasa su samu ƙwarewar fasahar zamani da za ta buɗe musu ƙofofin samun aikin yi bayan kammala NYSC.

Kowane wanda aka amince da buƙatarsa zai samu N10,000 a matsayin kuɗin shiga shirin da kuma N150,000 na kuɗin karatu, wanda jimlarsa ta kai N160,000.

Yadda ake neman tallafin

A sakon da ya wallafa a X, Sam Otigba ya ce masu sha'awar shiga shirin za su fara ziyartar shafin neman tallafin na NYSC da ke nan.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta kashe N500m a kare martabar Najeriya kan zargin gallazawa kiristoci

Bayan haka, za su cike fom ɗin neman tallafin tare da bayanan NYSC ɗinsu sannan su zaɓi shirin Diploma na AltSchool Africa da suke son karantawa.

Daga nan sai su tura buƙatarsu domin tantancewa. Idan aka amince da su, za su samu jagora kan yadda za su fara karatun tare da tallafin karatu.

Masu shirya shirin sun kuma bayyana cewa waɗanda ba su da kwamfutar tafi-da-gidanka za su iya neman ƙarin tallafin kwamfuta ta wata buƙata ta daban bayan sun nemi tallafin karatu.

masu bayar da tallafin karatu
Wadanda za su ba 'yan Najeriya tallafin karatu. Hoto: @SamuelOtigba
Source: Twitter

Waɗanne fannoni za a koyar?

Masu cin gajiyar shirin za su iya zaɓar daga cikin darussa daban-daban da suka haɗa da fasahar AI a fannonin daban-daban.

Haka kuma akwai harkokin kasuwanci na zamani a cikin shirin, waɗanda ake buƙata sosai a duniyar yau.

Baya ga horon fasaha, masu cin gajiyar shirin za su samu damar aikin horaswa, taimakon neman aiki ta Jobs59, shawarwari kan gina sana'a da kuma yadda za su gina rayuwarsu..

Za a ba da bashin kwamfuta

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta buɗe neman shiga shirin C.L.I.C.K.D. domin bai wa 'yan Najeriya damar samun kwamfutoci da sauran na'urorin dijital.

Kara karanta wannan

Kano ta canja salo, an ɗauki sabon mataki don yaƙi da shaye shaye da daba

Shirin wanda CREDICORP ke gudanarwa tare da Ma'aikatar Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Dijital, zai ba masu cancanta damar samun kwamfutocin tafi-da-gidanka, wayoyin zamani da tablet ta hanyar tsarin biyan kuɗi cikin sauƙi.

A matakin farko, shirin ya fi mayar da hankali kan mahalarta shirin 3MTT, amma an kuma nuna cewa masu alaƙa da AltSchool Africa, ALX, Andela na iya amfana a matakai na gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng