Kano Ta Canja Salo, An Ɗauki Sabon Mataki don Yaƙi da Shaye Shaye da Daba

Kano Ta Canja Salo, An Ɗauki Sabon Mataki don Yaƙi da Shaye Shaye da Daba

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da kwamitin haɗin gwiwa domin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da daba da su ka addabi jihar Kano
  • lhaji Abba Kabir Yusuf ya kuma sanya hannu kan wani sabon umarni domin ƙarfafa yaƙi da kungiyoyin daba da sauran ayyukan ta'addanci a fadin Kano
  • Gwamnatin Kano ta ce za ta samar wa kwamitin kuɗi, motocin aiki, ofisoshi da sauran kayan tallafi domin ba wa kwamitin damar ya gudanar da aikinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da wani kwamitin haɗin gwiwa na hukumomi daban-daban domin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Bayan samar da kwamitin, gwamnan ya kara da sanya hannu kan wani umarnin zartarwa da zai ƙarfafa matakan yaƙi da daba da sauran ayyukan laifi a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya bayyana matsayar Kano kan kafa 'yan sandan jiha

Gwamnatin Kano ta tashi a kan daba da shaye-shaye
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yayin wani taro a jihar Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

The Punch ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba, 22 ga watan Yuli, 2026.

Gwamnan Kano ya tashi kan shaye-shaye

A rawayar jaridar Daily post, Gwamnan ya bayyana cewa shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na daga cikin manyan ƙalubalen da ke barazana ga matasa a Kano.

Ya ce wannan matsala tana haddasa aikata munanan laifuffuka, rusa iyalai, tauye ci gaban tattalin arziki tare da kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Gwamna Yusuf ya bayyana cewa sabon kwamitin zai jagoranci dukkannin matakan gwamnatin jihar wajen magance matsalar ta hanyar tattara bayanan sirri, aiwatar da doka, wayar da kan jama'a.

Gwamnan Kano ya ce an tanadi kayan yaki da daba a jiharsa
Gwamnan Kano sanye da kayan jami'an tsaro a jihar Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Haka kuma gwamnan ya bukaci kwamitin da ya kula da masu fama da shaye-shaye da kuma yin aiki tare da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya ce:

"Sabon kwamitin da aka ƙaddamar zai jagoranci matakan gwamnatin jihar na yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ta hanyar tattara bayanan sirri, aiwatar da doka, wayar da kan jama'a, gyaran halayen masu shaye-shaye da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki."

Kara karanta wannan

"Ya fi su": Gwamna Sule ya fadi fannin da Tinubu ya yi wa Atiku, Obi fintinkau

Gwamnan Kano ya karfafi kwamiti

Gwamnan ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta samar wa kwamitin isassun kuɗI, motocin aiki, ofisoshi, kayan aiki da kariyar tsaro, tare da ba shi damar gudanar da aikinsa cikin 'yanci ba tare da katsalandan ba.

Ya kuma ce gwamnati na ci gaba da faɗaɗa cibiyoyin gyaran masu shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, yana mai bayyana cewa an riga an samar da cibiyoyi daban-daban na maza da mata domin kula da masu fama da wannan matsala.

A cewarsa, umarnin zartarwar da ya sanya wa hannu zai ƙara ƙarfi ga ƙoƙarin gwamnati na tarwatsa ƙungiyoyin daba, rage rikice-rikicen siyasa masu ɗauke da tashin hankali da kuma tallafawa hukumomin tsaro.

Shugaban kwamitin, Barrista Muhuyi Magaji Rimingado, ya gode wa gwamnan bisa amincewar da ya nuna masa da sauran mambobin kwamitin.

Gwamnati ta shirya kafa yan sandan jiha

A wani labarin, kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce Kano ta shirya tsaf domin kafa rundunar 'yan sandan jiha yayin da ake samun masu aikata laifuffuka a lungu da sako jihar a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Pantami na shirin 2027, gwamna ya rantsar da sababbin kwamishinoni 23 a Gombe

Gwamnan ya kuma bayyana irin alaƙar da runduna za ta yi da ta 'Yan Sandan Najeriya idan an kammala kafa ta, ba wai za ta maye gurbinsu za a yi ba, illa za a yi aiki tare domin tsaftace Kano daga masu aikata laifi.

Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da goyon bayan duk wata hanya da za ta inganta tsaron Najeriya domin samun sauki, yayin da ya ce Kano na da duk abin da ake bukata wurin kafa rundunar

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng