NYSC: Surutu Yayi Yawa Minista Ya Canza Magana game da Sauya Khaki da Adire
- Gwamnatin tarayya ta yi maza ta karyata rahoton da ake ji cewa masu bautar kasa za su rika sanya kayan atamfa nan gaba
- Ayodele Olawande ya ce Gwamnatin tarayya ba ta kai ga maye gurbin khakin da aka saba gani a a NYSC da tufafin adire ba
- A wani kokarin haske, Ministan matasan Najeriya ya tabbatar da cewa misali kurum ya bada wajen bayanin sauyin da aka kawo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Ministan cigaban matasa, Ayodele Olawande, ya yi karin haske game da batun canza kayan da masu bautar kasa suke sanyawa.
A ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli 2026, ministan ya fito ya fayyace hakikanin halin da ake ciki ganin yadda jama’a suke ta surutu kan batun.

Source: Getty Images
Ministan matasa ya fitar da sanarwa a X
Ayodele Olawande ya yi amfani da dandalin X da aka fi sani da Twitter yake cewa ba a kai ga amince da amfani da Adire a NYSC ba.
Ministan harkokin matasan ya ce ba a fahimci abin da yake nufi ba ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin cikin tsakiyar makon nan.
Saanarwar ta tabbatar da cewa zuwa yanzu hukuma ba ta kai ga amincewa a maye gurbin kayan sojoji na khaki da wata atamfa ba.
"Niyya ta ita ce kawai in kawo misalan wasu daga cikin shawarwarin da aka kawo yayin tattaunawarmu.
Ba sanarwa ba ce cewa an yi na’am da wani nau’in tufafi ko kuma cewa an amince da kayan da za su canji khakin NYSC.”

Source: Getty Images
Wani tufafi masu NYSC za su sanya?
A cewar ministan, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tana duba duk shawarwarin da aka gabatar, kuma za ta zabi wanda ya fi dacewa da matasan.
Jawabinsa ya kuma ce gwamnati za ta duba kayan NYSC da zai fi dacewa da yanayin Najeriya, karko, amfani, araha da kuma nuna kishin kasa.
Punch da ta bibiyi jawabin ministan ta ce ya yi kira ga jama’a da cewa kar su bari zancen tufafin masu bautar kasa ya shafe jerin sauyin da aka yi.
An yi wa tsarin NYSC garambawul ne saboda a bunkasa kasuwanci, kara damar samun ayyukan yi, habaka kishin kasa da kuma shiga fagen aiki.
Minista ya ce NYSC za su koma atamfa
A lokacin da aka yi hira da shi a tashar talabijin, Olawande ya nuna za a koma amfani da adire. Amma da alama mutane ba su natsu da kayan ba.
Masu korafin sun ce adire ya fi kama da tufafin wata kabila kuma khaki ya fi kwari kuma kaya ne da zai dace da mata da maza, ga shi launin Najeriya.
Hujjar da ya kafa ita ce anyi hakan ne domin amfani da atamfar Najeriya zai habaka masana’antun tufafi kuma gwamnati ta rage facaka da kudi.
NYSC ya gamu da manyan sauye-sauye
Rahoton nan ya ce Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta amince da gagarumin garambawul ga tsarin bautar kasa na NYSC a karon farko tun shekarar 1973.
Wannan sabon sauyi na da nufin samar wa matasa kwarewa da fasahohin zamani domin ba su damar fuskantar kalubalen rayuwa da bunkasa tattalin arziki.
Daga cikin gyare-gyaren har da sauya tsofaffin kayan khakin NYSC zuwa tufafin kamfala (Adire) da kuma tura matasa wuraren aiki gwargwadon fannin karatunsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

