Bayan Korar Kwamishinoni, Gwamna Sule Ya Sallami Hadimansa daga Aiki
- Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya sauke masu ba shi shawara na musamman guda takwas daga mukamansu
- Ya naɗa sabbin masu ba shi shawara na musamman guda tara bayan kwana biyu da sauke kwamishinoni shida
- Sababbin masu ba shi shawarar za su kula da fannoni daban-daban a ƙananan hukumomi tara na jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Lafia, jihar Nasarawa - Kwana biyu bayan sauke kwamishinoni shida daga mukamansu, Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya sauke masu ba shi shawara na musamman guda takwas.
Gwamna Sule ya kuma naɗa wasu masu shawara guda tara, lamarin da ya ƙara nuna ana sake fasalin majalisar zartarwar jihar.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce an bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Nasarawa, Shuaibu Magaji Labaran (SAN), ya fitar ranar Juma’a, 24 ga watan Yulin 2026.
Labaran ya ce gwamnan ya bayyana cewa matakin na daga cikin ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da ƙarfafa ayyukan hidima a faɗin jihar.
Waɗanda aka sauke
Waɗanda aka sauke daga mukamansu sun haɗa da Hon. Lawal Yakubu Karshi, Hon. Danlami Lawal Moroa, Haruna Kasimu Idris.
Sauran su ne Hon. Gambo Abdullahi, Muhammadu Usman Shege, Ibrahim Shekarau Dahiru, Engr. Moses Utondo da Hon. Elsie Monday.
Sababbin masu ba Gwamna Sule shawara
Sai dai Gwamna Sule ya amince da naɗa sababbin masu ba shi shawara na musamman guda tara, waɗanda za su kula da fannoni daban-daban tare da wakiltar wasu ƙananan hukumomin jihar.
Sabbin waɗanda aka naɗa su ne Barr. David Moyi Sule, mai ba gwamna shawara kan ayyukan jin ƙai, daga Obi; Hon. Jafaru Ango, mai ba gwamna shawara kan ayyukan jama’a, daga Karu; Alh. Ado Dauda, mai ba gwamna shawara kan zuba jari a harkokin jin daɗin jama’a, daga Kokona; da Hon. Abdullahi Angibi, mai ba gwamna shawara kan harkokin siyasa, daga Lafia.
Sauran su ne Hon. Prince Nuhu Dauda Shege, mai ba gwamna shawara kan raya karkara, daga Toto; Hon. Joseph Attah, mai ba gwamna shawara kan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, daga Doma; Dr Felix Upav Saaior, mai ba gwamna shawara kan ilimi, daga Obi; Hon. Peter Mbucho, mai ba gwamna shawara kan lafiya, daga Akwanga; da Idris Suleiman Dansauka, mai ba gwamna shawara kan harkokin sarauta, daga Keffi.
Sanarwar ta ƙara da cewa za a sanar da ranar rantsar da sababbin masu ba gwamnan shawara a lokacin da ya dace.

Source: Facebook
Gwamna Sule ya kare Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, ya kare ƙoƙarin shugaban Bola Ahmed Tinubu na sake tsayawa takara.
Gwamna Sule ya ce tarihin aikinsa ya fi na sauran masu neman shugabancin ƙasa a zaɓen 2027 nesa ba kusa ba.
Gwamnan ya ce banbancin da ke tsakanin Tinubu da abokan hamayyarsa ya yi kama da “dare da rana”.
Asali: Legit.ng

