An Yada Bidiyon Trump Ya Dungura Kasa yayin Shiga mota, Shin da Gaske ne?
- An yaɗa wani bidiyo a shafukan sada zumunta da ke ikirarin cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya faɗi yayin da yake ƙoƙarin shiga motar shugaban ƙasa
- Masu binciken gaskiya sun bayyana cewa bidiyon ba na gaskiya ba ne, an ƙirƙire shi ne ta hanyar amfani da fasahar AI domin ya nuna abin da bai faru ba
- Rahotanni sun nuna babu wata kafar yaɗa labarai mai sahihanci da ta tabbatar da cewa Trump ya faɗi ko ya suma a kwanakin nan kamar yadda aka yaɗa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Wani bidiyo da ya bazu sosai a shafukan sada zumunta ya jawo ce-ce-ku-ce bayan an yi ikirarin cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya faɗi yayin da yake shiga motar shugaban ƙasa.
Rahotanni sun nuna cewa an fara yaɗa bidiyon ne a ranar Juma'a tare da rubuce-rubucen da ke cewa Trump ya dungura ƙasa yayin shiga motarsa, lamarin da ya sa wasu suka fara tambayar ko yana da wata matsalar lafiya.

Kara karanta wannan
Trump ya lallaba ya tura bukatar tsagaita wuta Iran ta Iraq, Tehran ta yi martani

Source: Getty Images
Sai dai binciken da Roya News ta gudanar ya nuna cewa ikirarin ba gaskiya ba ne, domin an ƙirƙiri bidiyon ne ta amfani da fasahar kirkirar hoto da bidiyo ta AI.
Bidiyon ba na gaskiya ba ne
Rahotanni sun bayyana cewa wani mai zanen barkwanci mai suna Oliver Markus Malloy ne ya fara wallafa bidiyon a shafin X a ranar 24 ga Yuli, 2026.
A cikin bidiyon mai tsawon kusan daƙiƙa 18, ana ganin kamar Trump ya yi tuntuɓe kafin wani jami'in tsaro ya taimaka masa ya shiga mota.
Sai dai bayan ƙarin bincike, masana da na'urorin gano bidiyon AI sun tabbatar da cewa an yi wa bidiyon kwaskwarima ne ta hanyar fasahar AI.
Sun bayyana cewa akwai alamun da ke nuna ba bidiyo na gaske ba ne, ciki har da motsin jiki da bai dace ba, tangarɗa a hoton mutane da motar, da sauran kura-kuran fasaha.
Ga bidiyon a kasa:
Karin bayani kan bidiyon
Binciken ya kuma nuna cewa babu wata kafar yaɗa labarai mai sahihanci, ko ta Amurka ko ta duniya, da ta ruwaito cewa Trump ya faɗi ko ya suma yayin wani taron jama'a a kwanakin baya.
Masana sun ce bidiyon ya yi kama da wani tsohon bidiyon da aka ɗauka a watan Nuwamban 2025 lokacin da Trump ya sauka daga jirgin Air Force One a Palm Beach.

Source: Getty Images
Masu binciken gaskiya sun bukaci jama'a su riƙa tantance sahihancin irin waɗannan bidiyoyi kafin su yaɗa su, musamman waɗanda suka shafi shugabanni da manyan mutane.
Trump zai kai hari Mali
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump, na nazarin yiwuwar kai hare-haren soji kan ƙungiyar JNIM mai alaƙa da Al-Qaeda a ƙasar Mali.
Rahotanni sun ce ana duba yiwuwar ɗaukar wannan mataki ne saboda hare-haren da ƙungiyar ke kai wa a Mali da wasu ƙasashen Afirka ta Yamma.
Idan aka amince da shirin, Mali za ta zama ƙasa ta takwas da gwamnatin Trump za ta kai wa hari tun bayan komawarsa kan mulki.
Asali: Legit.ng
