An Rike Dan Ta'adda da Ya Nufi Fadar Sarki da Bindiga zai kai Hari

An Rike Dan Ta'adda da Ya Nufi Fadar Sarki da Bindiga zai kai Hari

  • Rahoto ya nuna cewa dakarun 'yan sanda sun dakile hari da aka nufa za a kai wata fada tare da kama mutum daya dauke da bindiga
  • Jami'an da suka kama mutumin sun kwato bindigar kuma an riga an fara bincike kan makamin da abokan da ake tunani ya hada kai da su
  • Kwamishinan 'yan sandan Akwa Ibom ya yaba wa jami'an tare da gargadin masu aikata laifuffuka cewa ba za su samu mafaka a jihar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Akwa Ibom - Rundunar 'yan sandan Jihar Akwa Ibom ta kama wani mutum mai shekara 42 da ake zargi da kutsawa cikin wata fada dauke da bindiga kirar gida a Karamar Hukumar Essien Udim ta jihar.

Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar, DSP Timfon John, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a Uyo ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka fatattaki 'yan ta'adda da suka kai hari sansanin sojojin Zamfara

Taswirar jihar Akwa Ibom
Taswirar jihar Akwa Ibom a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Punch ta wallafa cewa sanarwar ta ce an kama wanda ake zargin, Bassey Udo Idiong, a ranar 1 ga Yuli, 2026, da misalin karfe 9:00 na dare bayan samun kiran gaggawa.

Yadda aka kama Idiong

Mai magana da yawun rundunar ta ce jami'an sun yi aiki ne bisa sahihan bayanan sirri, inda suka garzaya wurin cikin gaggawa, suka kwace bindigar daga hannun wanda ake zargin tare da kama shi.

Sanarwar ta ce rundunar ta samu wani gagarumar nasara a yakin da take yi da aikata laifuffuka, bayan kama wanda ake zargin da aikata laifin dauke da makami tare da kwato bindiga kirar gida a Essien Udim.

Ta bayyana cewa, a ranar 1 ga Yuli, 2026, da misalin karfe 9:00 na dare, cibiyar karbar korafe-korafen rundunar da ke Uyo ta samu rahoto daga wani mutum da ba a bayyana sunansa ba.

Rahoton ya bayyana cewa Bassey Udo Idiong, mai shekara 42 ya shiga fadar wanda ya yi kiran dauke da bindiga kirar gida tare da yi masa barazanar harbi.

Kara karanta wannan

Rikicin kabilanci ya barke a Niger, an kona mutane da ransu

An kwace bindga a fada

Bisa wannan bayani, jami'an rundunar sun isa wurin cikin gaggawa, suka kwace bindigar daga hannun wanda ake zargin ba tare da wani tashin hankali ba, sannan suka kama shi tare da kwato bindigar a matsayin hujja.

Rundunar ta ce wannan mataki ya hana afkuwar wani mummunan lamari da zai iya jawo asarar rayuka, tare da nuna kudirinta na mayar da martani cikin gaggawa ga duk wata barazanar tsaro a jihar.

'Yan sandan Najeriya a wajen taro
Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya a wajen aiki. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Za a gurfanar da wanda ya je fada

DSP Timfon John ta ce wanda ake zargin yana tsare a hannun 'yan sanda, yayin da aka fara bincike domin ko akwai wasu abokan huldarsa ko kungiyar masu laifi da ke da alaka da shi.

Ta kara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Mai magana da yawun rundunar ta ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Baba Mohammed Azare, ya yaba wa jami'an da suka gudanar da aikin saboda kwarewarsu da kuma saurin daukar mataki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa masu koyon karatun Alkur'ani wuta a Bauchi

Dannau ya danne 'yan bindiga

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu mutane 11 da 'yan bindiga suka kama sun kubuta bayan tafiya da su cikin wani daji mai zurfi.

Daya daga cikin mutanen da ya kubuta ya bayyanawa manema labarai cewa dannau ne ya danne 'yan ta'addan su kuma suka samu kofar guduwa.

Rundunar 'yan sandan jihar Edo ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da sanar da cewa ta kama mutane da dama da ake zargin suna garkuwa da mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng