Jirgin Sama Dauke da Turawa 11 Ya Yi Hatsari a Amurka, Ya Kamata da Wuta
- Wani jirgin ruwa mai saukar ungulu dauke da mutum 11 ya yi hatsari a kusa da tsibirin Sucia, inda aka ceto dukkan fasinjoji cikin gaggawa
- Shaidu sun bayyana yadda jirgin ya sauka da karfi a ruwa kafin ya bugi duwatsu, sannan wuta mai karfi ta kama jirgin gaba daya
- Hukumar FAA ta fara binciken musabbabin hatsarin, yayin da kamfanin jirgin ya dakatar da dukkan zirga-zirgarsa na ranar Juma'a domin bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Amurka - Wani jirgin ruwa mai saukar ungulu da ke dauke da mutane 11 ya yi hatsari kusa da wani tsibirin yawon bude ido da ke arewacin birnin Seattle.
Rahoto ya nuna cewa jirgin ya kama wuta tare da jawo dauki-dai daga jami'an tsaro wajen ceto fasinjojin da suka jikkata da matukin jirgin zuwa asibiti.

Source: Getty Images
Jirgin sama ya yi hatsari a Amurka
Bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna jirgin na karkata gefe daya yayin da yake tashi a kan ruwa kusa da wasu jiragen ruwa da ke gabar teku, in ji rahoton CBS News.
Jirgin ya yi saukar gaggawa kafin ya yi karo da wani babban dutse dake gabar teku.
Shaidun gani da ido sun yi gaggawar zuwa domin bayar da taimako yayin da hayaki ya fara tashi kafin wuta ta cinye jikin jirgin da ya tsaya a kusa da babban dutse.
Hadurran jiragen ruwa a Amurka
Hukumar Tsaron Teku ta Amurka ta bayyana cewa an fitar da sanarwar gaggawa ga masu zirga-zirgar ruwa a yankin, kuma jiragen agaji da dama sun amsa kiran domin bayar da taimako.
Hatsarin, wanda ya shafi matuki da fasinjoji 10, ya faru ne makonni biyu bayan wani jirgin makamancin haka ya yi saukar bazata a wani kogin New York tare da haifar da raunuka marasa tsanani.
A shekarar 2022, hukumar ta ba da umarnin duba irin wadannan jiragen bayan wani hatsari da ya faru a ruwan Puget Sound dake arewa maso yammacin Seattle.
Hatsarin na ranar Alhamis ya faru ne a yankin Shallow Bay kusa da tsibirin Sucia dake yankin San Juan. Wannan yankin na da shahara wajen harkar yawon bude ido da sha'awar kallon kifi da kuma yawo.

Source: Getty Images
Bayanin kamfanin jirgin
Shugaban kamfanin jiragen saman na Kenmore Air, David Gudgel, ya bayyana godiyarsa kan cewa an samu tsira da dukkan mutanen da ke cikin jirgin a lokacin da hatsarin ya faru.
Ya kara da cewa kamfanin ya soke duk wani jirgin da ya kamata ya tashi a ranar Juma'a kuma suna ba da goyon baya ga masu gudanar da bincike kan abin da ya haddasa hatsarin, in ji rahoton BBC.
Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta tarayya ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike domin gano takamammen abin da ya haifar da matsalar da ta jefa jirgin cikin hatsari.
Jirgin soji ya yi hatsari a Amurka
A wani labari, mun ruwaito cewa, mutane takwas sun mutu bayan wani jirgin yaƙi na rundunar sojin saman Amurka kirar B-52 ya faɗi nan take bayan tashinsa a Kudancin California.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:20 na safe agogon yankin a ranar Litinin yayin da jirgin ke gudanar da aikin gwaji na yau da kullum.
Rahoto ya nuna cewa hatsarin ya kasance a cikin yankin sansanin sojin sama na Edwards a kan titin tashin jirage, kuma an dakatar da ayyukan sansanin na ɗan lokaci.
Asali: Legit.ng


